11Duduwa ta bude zip din lalitar jikinta ta zaro yar guntuwar goronta ta Balla sanan ta amsa”waalaika salamu,higo” ta shigo cikin gidan jikinta na rawa “Duduwa ina wuni”, da sauri Duduwa ta ijiye tabaryan hannunta ta mike tsaye baki abude tana kallon Rufaida, ” bakar mayya mekika dawoyi? Kindawo kasheni ne nima? Kin kashe Dana Musa da matarsa Asiya shine yanzu kika biyoni nima ki kashe” Rufaida ta tsaya tana share kwalla tace “wlh banina kashe suba Duduwa,gini ne yafado akansu” da sauri Duduwa tace “to dan ubanki juya kibar gidana,dama ai duniya kika shiga ki koma Chan inda kika fito ki barmin gida,Alhamdulillah dama Wanda ya kawoki ya mutu dan haka babu Wanda ya isa yanzu yahana ni koranki, wuce kibarmin gida” kuka tafashe dashi sosai tazo dagudu ta tsugunna agaban Duduwa ta dan Allah Duduwa karki koreni babu inda zani banda kowa wlh” ta hankada ta”,sakenmin kafa, da Chan dakika shiga duniya dawakike tare,kina gidan karuwai ko?” ta girgiza kai tace “A’a, dan Allah Duduwa kibarni na zauna”, Duduwa ta turata da kafa ta fadi “dan ubanki tashi ki barmin gida bazan iya zama da karuwa irinki ba, nizaki rainama wayau kafin a haifeki da shekaru dari nake duniya,daga ganin yanda kikai danya danya dinan kinwaniyi huras(fresh) cikin shegema gareki” ta finciki tabaryan datake daka fura dashi tace “tashi ki barmin gida” da gudu ta mike tayi hanyar fita tana kuka kaman za’a zare ranta, Duduwa takoma tacigaba da dakanta tana sauraran yanda Rufaida ke banka uban kuka, kome ta tuna sainaji tace “Faida” da sauri Rufaida dake kuka a zauren tace “naam” Duduwa tace “yaki” ta shigo, “dau tulu kije ki dibomin ruwa a rafin,idan kin gama ciccika randunan saikije ki gyara bukkan Chan shine dakinki” ta nuna mata wani bukkan Kara,da ake ajiye tumakai aciki da.
Murmushi tadanyi saboda dadin Allah ya daurata kan Duduwa zata yarda ta zauna,”bazaki wuce ki dauki tulu ki tafi ba shegiya mai kama da ifiritu”cewar Duduwa, da sauri taje kusa da kitchen tadau tulu ta juya zata tafi Duduwa tace “zonan” taje gaban Duduwa tana dar dar,mekuma tayi?
wukar dake gefen Duduwa ta dauka saida Rufaida taji tsoro Duduwa tasa wukan ta kyasta hijabin dake jikinta tundaga sama har kasa tana masifa “da da wanan shegen kimar(dogon hijabi) dinan zaki fita, shegiya rubabbiya, bakisan aurar dake zanyiba,kinwani sa wanan abun wazaiga jikin naki haryaso,wlh duk randa nakara ganin kinsa kimar kin fita saina kusa kasheki da duka,wuce daki zakiga wani tsumma danake goge kasa ki dauka kisa ki cire wanan na jikinki,anjima idan dillaliya tazo na siyar nasamu kudin saro sabuwar gyara”.
Ranta baiso ba,dan taso ta dinga tuna mutumin daya taimaketa ta hanyar ganin wanan doguwan rigan mai kyau kullum,chanza kayan tayi tasa tsumman da Duduwa tace sai warima suke hakanan tafito tadau tulun tace “Duduwa natafi” ko kallonta Duduwa batayi ba kirga fura take. Tajuya tafita tana tafiya ahankali, daga gidansu zuwa rafi badai nisaba,dan kusan karshen kauyen rafin yake.
Barr Barraq babu inda baije ba agarin Minna neman taba,hatta inda ya tsinceta saida yaje,ranshi yabaci iya baci,yanzun ina taje? Ina ta shiga? Ga dukiyarta a hanunshi yazaiyi da ita? yunwa yasa ya kalli agogo yaga karfe 4 na rana a bakin wani masallaci ya paka yay salla sanan yabiya wani eatery yasai meat pie da Vita milk, dawowa mota yayi ya zauna ya dauko meat pie din zaici jiyayi ya tsani meat pie din yay wurgi dashi ta glass din mota, ya kunna taba kawai yaja motan yay gaba hotel yakoma su Johnson namishi magana ko kulasu baiyiba ya wuce dakinshi ya fada kan gado. Saikuma ya tashi yadauko wani karan taban yasha sanan yadanji bacin ran yaragu. wani dan abu naga ya danna a gefen gadonshi saiga Solomon ya shigo ahankali yace “kiramin P.A” ba adadeba PA ya shigo, Barr ya kalleshi yace “PA inaso kaje banki ka bude new account ka zubamin wanan kudin aciki,gobe ne zamu koma Abuja, bazamu iya komawa yauba” PA ya amsa da to yadau Ghana masgon da yaga Barr na nunamishi yafita daga dakin, tashi yayi yawuce yay wanka.
Sai Wuraren issha tagama cika randunan da Duduwa tace ta cika,ta gaji iya gajiya taje zata dibi ruwa taje tai wanka taga Duduwa ta haskota da tocula ” mezaki min da ruwa?”da sauri ta rufe randar tace”dama wanka zanyi” Duduwa cike da masifa tace” akace miki wanan ruwan na wankan ki neko,shegiya mai kama da ifiritu,idan zakiyi wanka kinsan hanyar rafi kuwuce kije ki debo,ruwan nan bana amfanin ki bane” ta tashi daga wurin tadau buta tai alwala, kallon dakin Duduwa tayi taga bata falo alamun tana uwar daka, da sauri taje dakin mamarta kafin subar kauyen ta shiga da kyar ta lalubo wani yamutsartsen hijabi hakanan tasa tai salla sanan tacire tafito ta zauna abakin kofan Duduwa tai shiru. gyangyadi na daukan ta saboda gajiyar datayi. Kwal taji anbuga mata wani abu abaya da sauri ta tashi tana Sosa wurin saboda azabar zafin dataji, Duduwa tace “wanan kazamtacciyar jikinki zaki wani kwantamin a tsaftatacciyar bakin kofana mayya, yi Chan” ta nuna mata gaban bukkanta,tajuya tana Sosa wurin da Duduwa tabuge ta tana kuka,”zonan! Duduwa ta daka mata tsawa “ungo”,Tamika mata ragowan tuwon dataci tarage,da sauri ta karba tareda fadin “nagode Duduwa”, taje gaban bukkanta ta zauna taci ko koshi batayi ba amma bata damuba tunda tama samu Tabata, ta tashi zataje tasha ruwa,harta bude randa Duduwa ta haskota da tocula “wlh inkika tabamin ruwa sainaci kan ubanki,kona alwala Dana bari kikayi shima dan ubangiji zakima ibada wuce kibar wurinan ki shige dakinki kiyi bacci”.
Da sauri ta shiga bukkan, ta zauna ta baki-bakin kofa,dan cikin bukkan duhu bata ganin komi,gashi kauyen ba wuta,tsoro takeji na bala’i. a zaunen tafara bacci sama-sama jin kaman kwaro nabin jikinta yasa tasaki ihun bala’i tafito tsakar gidan tana ihu, da sauri Duduwa tafito daga dakinta tana Kara gyara daurin zani ta daura mata dundu abaya tace ” shegiya bakar mayya,to wlh Kinyi kadan kihanani bacci, lpy kikemin ihu?” Da kuka tace “Duduwa kwaro kebin jikina wlh” Hannunta Duduwa taja ta haska dakin da tocula duk kyankyasai na bayi kebin kashin ragunan wurin,Rufaida takara ihu tarike Duduwa tace “kingansu kk Duduwa” Duduwa ta hankadata ciki,ta jawo kofan bukan ta rufe tana masifa “dan ubanki su cinyeki,Allah sama ki mutu kaman yanda kika kashemin Dana da matarshi”, ta ciro kwado daga lalitar jikinta tasa tajuyo tanajinta tana ihu amma ko das bataji arantaba, saima masifar data cigaba dayi “Marigayi Musa bakajin magana, kawai ka tsinto yarinya ka tsinto jaraba,gashinan ta hanani yin bacci,to wlh duk maitarta Ni bata isa ta lasheni ba, yanda kika kashemin da Ni da wahala zan aikaki barzahu” tahau yar gadon bunun ta ta kwanta,tana korafi.
Rufaida dataga ihu da jijjiga kofa bazai fisheta ba saita make ajikin kofan tama kasa hawaye,Umma tafado ranta,””lokacin kafin Abba yasamu aiki subar kauye suje Minna Duduwa ta taba kulleta a wanan dakin lokacin tun ragunan ma naciki,haka Abba da Umma suka roketa amma taki budeta,Umma tadaga haka saitazo ta tsaya a bakin kofan tace Rufaida ki dinga fadin A’uzubikalimatillahi tammat min kulli sha’in ma kalaq” tunawa da addu’a da Umma takoya mata yasa tafarayi ahaka har bacci ya kwasheta Wuraren karfe 1 na dare batare dataji kwaro yahau jikinta ba ko wani abu ya cijetaba.
Karfe 5 na asuba taji an zaulamata zabori a cinya, a firgice ta mike tsaye taga Duduwa ce, tace”Ina kwana Duduwa ” Duduwa ta kalleta shekeke tace” karuwa,watoma yanzu baccin karuwai kikemin a gidako? Bacci babu zani a jikinki”da sauri tadau zaninta daya warware saboda nauyin bacci ta daura,Duduwa tace “wuce ki share tsakar gidan nan tass,sanan kidau gero ki surfa na fura,wuce kitafi kin tsàya kina kallona” da sauri tafita daga bukkan tana daga kafanta da kyar saboda mugun ciwon maran datake ji, haka takarasa sharaan gidan ko salla Duduwa bata bari tayiba tamiko mata geron tace “ungo surfe min su” ta karba ta yayyafa ruwa ta juye a turmin tafara surfewa Duduwa ta wuce daki danshan kokon ta da kosai.
Jin cikinta na ciwo sosai yasa ta rike tabaryan ta tsugunna a wurin tana cije lebe, ahankali taji abu nabin cinyoyinta wanda tasan tabbas bakon watan natane,cusa kanta tayi a cinya tana cije lebe saboda zafin ciwon Mara,tanajin jini nabin jikinta amma to mezatayi,Abba da Umma masu siyan mata audugar mata(always) basa duniyar yanzu,kuka takeyi ahankali saboda kar Duduwa taji.
Duduwa ce ta fito daga dakinta “ke mekikeyi a tsugunna ba surfe nasakiyi ba”, mikewa tsaye tayi tace “Duduwa cikina ke ciwo”
Da sauri Duduwa tace “to kimutu mana,ganin abu kaman jini jini a kasan wurin yasa Duduwa karasowa wurin da sauri tabi zanin jikinta da kasan wurin da kallo tafara tafa hannu tana salati tana sallallami”Faida” ta ambata tareda rike haba,tacigaba ” habawa ni dama nace karuwan ci kikeyi,dama naga alamun kinada ciki jiya,shine yanzu kikazo gidana kina bari?” Rufaida takara tsugunna wa saboda ciwon cikin datakeji, duka Duduwa tarufeta dashi tana kuka yanzu dama ciki kikaje kika dauko yarnan,shine kikemin bari a gida,nida nake shirin aurar dake, saida tagaji da dukanta sanan ta saketa ta mika mata tulu,wuce kije rafi ki debomin ruwa kuma wlh ahaka zaki tafi saina tona miki asiri,duniya tasa cikin shege kikayi yar iska,haka Rufaida tafita daga gidan tana kuka jikinta da zaninta dukya baci,sai kallonta ake, haka taje tadawo tajuye takoma nabiyu,kuka kawai take ahanya ita bama kukan ana kallonta take ba kukan yanda jikinta yabaci take haka taje rafin tadebo ruwa tajuyo tana tafiya ahankali jin tafiya na neman gagaranta yasa ta sauke tulun ta tsugunna akan hanya ta rike cikinta wayyo cikina. Rufaidatu taji anfada da sauri ta dago kanta taga Baba ne, yadanyi murmushi “Ashe kece yata,me kikeyi anan wurin kin tsugunna,a’a tashi mana yata”,ahankali ta tashi kallon kafanta yayi yaga jini wani nabin wani ga zanin jikinta tama haka da sauri ya sakko daga kan amalanken yazo kusa da ita ya dafa kanta “Rufaidatu menene? Maiya sameki? Wanan jinin dakebin kafanki fa” kuka tafashe ma Baba dashi sosai tanajan numfashi “Baba cikina ke ciwo,Duduwa tace wai bari nakeyi” takarasa maganan tana kuka, Baba ya share hawayen idonta yace “ba bakon watanki bane?” Ta sunkuyar da kanta tana hawaye, daukan tulun ruwanta yayi ya daura akan amalanken yace “hau muje gidana ki gyara jikinki yata” da kyar ta iya hawa, ya duba aljihun shi yaga dagashi sai naira hamsin ya ciro yabata yace “gashi ki rike ki ajiye duk rana irin haka kyayi amfani dashi kina siyan magani kinji idan kuma inanan kizo wurina nabaki sayawa kisha, yanzu muje gidana Maman talatu tabaki magani” yahau suka tafi.
Source Maman Abd Shakur