Da sauri ta tashi ta rungume Hafsat tana mai tsanin farin ciki. Hafsat ta dagota da sauri”Anty Rufaida jikin ki zafi sosai, baki da lafiya ne?” Ta girgiza kai “ni wurin mummy zani, banason gidanan, plz kicema Uncle B ya maidani wurin Mummy kinji, plzzzz” ta kifa kanta akan cinyar Hafsat ta saki kuka. Ahankali Hafsat ke shafa bayanta “Rufaida ke matar aure ce,gidan mijinki shine gidanki, dakinki,rufin asirin ki, da martabar ki, masu iya magana suna kiran aure da YAKIN MATA,dudda Mum mamarki ce amma bazataji dadi taganki har kinzoba kwata kwata kwananki nawa da dawowa nan? ai seta zata kunyi fada ne,ko wani abun ya faru ko…” Rufaida cikin kuka tace “ai wani abunne yafaru, wlh uncle B mugu ne sosai Anty, ni gaskiya wurin Mum zan koma” Hafsat data gane abunda Rufaida ke nufi saitai murmushi “Anty Rufaida auren kenan, kowace wace undergo hakan,so is normal, zancema Uncle B asaki a islamiyyan da Muzzammil yasani”. Rufaida ta girgiza kai”Banason islamiyya, idan naji ana karatu kaina na ciwo bazan shigaba!. Ahakadai suka cigaba da hiran har daya tayi atare suka shiga kitchen bayan Rufaida ta gaida Muzzamil. Ahankali Muzzamil yace “B call Dr, ur Ajiya need a Dr kaga yanda take tafiya”. Barraq yadan saci kallonta hanunta rike da spatula a kitchen, yadawo da kallonshi ga Muzzamil a raunane yace”bazata yarda ba,fushi take dani,wlh I don’t know abunda zanyi,ta hargitsa min tunani gabaki daya,but is not my fault I need her dat time badly”. Muzzamil pat his shoulder ahankali yace”calm down,is normal fushin datake,nasan yanda kakeji, just give her some time zata huce, karamar yarinya ce kaine zaka koyamata komi” Barraq ya sauke ajiyan zuciya yace” to,ran Monday zanyi resuming office “. Sai 7:00 na yamma sukabar gidan Barraq ya wuce masallaci. Sai wuraren 9 ya shigo gidan sama yahau ya tura kofar dakin Rufaida ganinta akwance yasa ya juya zai fita da siririyar muryarta takirashi “Uncle B” juyowa yayi da sauri hannu ta mika mishi ya rike da sauri ya karaso ya zauna kusa da ita “jikin ki zafi Baby na nakira Dr?” Ahankali ta dagamai kai,tai rau-rau da ido “promise bazaimin allura ba” murmushi yayi yace”naji bazan bari amiki allura ba”. Zamowa Tayi ta tsugunna agabanshi ta hada hannayeta biyu takai wurin bakin ta “Uncle B plz forgive me, bazan Kara cewa ka kaini wurin Mummy ba, I was rude I know, plz forgive me kaji”takarasa maganan tana kuka. Barraq ya girgiza mata kai ya mika hannu ya dagota “is ok yawuce, bakimin komiba kinji baby na,we are good”. Kwalalo ido tayi ta kalleshi wot?ya tambaya,”plz karka karamin abunan na jiya ,is too painful, banaso plz” shiru yayi nayan sakanni yana tunani I was happy baby na tai magana batare data sako any childish abuba, amma gashi tasako, alright lemme answer yhu in a childish way too. Gyara gashin kanta yayi ya shafa kumatun ta”ok my Rufaida, bazan karaba, but duk randa kikai rashin ji,ko kika batamin rai,hmmm ranan sainayi ” da sauri ta kankame shi tana kukan shagwaba “Allah ni bazan ma rashin jiba I promise”. knocking akayi yasa ya tashi “I guess d doctor is here” fita yayi ya shigo da likitar. Yabasu wuri ta duba Rufaida magunguna ta rubuta musu tareda mishi fada akan yanda yabita sanan ta musu sallama ta tafi. Maman Abd Shakur
Misalin karfe 2:00 na rana Barraq ya shigo gidan sanye da suit baki hanunshi dauke da briefcase, yayinda PA ke biyedashi abaya suka shigo gidan PA ya zauna akan kujera yana karema gidan kallo, Barraq yace “bari nakira madam ku gaisa” PA yace to to. Barraq yay sama dan kiran Rufaida.
Dakinshi yafara shiga yay shower agurguje, ya sauya kaya zuwa na shan iska three quater da white shimi kal yana mamakin me baby keyi dabata ji shigowan shiba. Turare ya fesa kafin yafito ya shiga dakinta sassanyar kamshin dakinta ya bugi hancinshi hangota dayayi akan gado tana bacci,ahankali tana sauke numfashi yasa yay murmushi turo kofan yayi yakarasa gaban gado yay tsaye yana karamata kallo sanye take da shimi yar karaama an mata zanen daisy ajiki pink,sai skin tight dogo fari, gashinta tai katon kalaba dashi. hannayen ta yakama ya rike kinyi kyau my angel. Yakara bakinshi akunnenta yace”wake up ga Mommy tazo” cikin bacci Rufaida taji ance Mummy da sauri ta tashi tana waige waige Mummy taga Uncle B a gefenta “Uncle B ina mummy na?” Shiru yay yana mamakin yanda Mum da Rufaida keson junansu. Dagata yayi muje PA yazo ku gaisa. Bayi ta shiga ta daurayo fuska Ya mika mata hijabi tasa tana turamai baki ya rike mata hannu yana dariya “naji naji anjima u will call mummy kuyi magana sanan” tai tsalle suka sauka. gaisar da PA tayi takawo musu abubuwan kwalama sanan takoma sama. Aranan da daddare Barraq yakaita shopping yasaimata waya mai kyau Apple da kaya suka biya gida suka gaida Amma da Dad Rufaida nata murna zatai waya da mummy.
Kimanin watan Barraq da Rufaida uku da sati biyu kenan da dawowar Su Abuja. Babu abunda yakara shiga tsakanin su,Barraq yay hakuri yana koyamata wani irin sonshi da shakuwan daya wuce misali dasukai kwanan nan. Rufaida tai kyau sosai,takara kiba ta cika dam ga yawan zazzabin safe datakeyi ga bacci tarasa meke damunta. Breakfast suka gama tana kusa da Barraq zaune take ta daura towel fari ajikinta ajiye spoon din hanunshi yayi ya shafa kanta “baby na yau da wuri zan dawo na kaiki hospital,banason wanan zazzabin dakikeyi every morning” ya debo kwai yakai bakinta kawar da fuska tayi ta yamuse fuska “banaso” “O haba my baby mekikeso to nadafa miki kafin na fita?” girgiza mai kai takara yi”zanci ragowan shawar mana najiya “Barraq ya girgiza kai “idan zan dawo I will branch nasiyo miki more shawarma tunda shikadai kikeso, plz don’t fall sick be strong kinji darling “ta gyada mai kai ya mike tsaye yadau briefcase dinshi kafin ya tsugunna ya sumbaci goshinta “I luv yhu, natafi” ya mike yay hanyar fita harya rike door handle Rufaida tace”uncle B “da gudu ta tashi tafada jikinshi tana kuka sosai duk sai shima yarude “baby na menene?”cikin kuka tace”am scared gabana faduwa yake since morning,bansan mesaba,plz stay,something is going to happen ” ajiye briefcase din yayi akan kujera ya kwanto da kanta kirjinshi yana shafa bayanta”Dear listen, nothing is going to happen, akwai enough securities, ga mai gadi babu abunda zai kamaki”. inada urgent case ne a supreme court yau daban fitaba,kuma yau mutumin nan na Lagos da matar shi wanda yarsu tabata zasuzo gaidamu, zan dawo da wuri, kije kiyi bacci kafin nadawo nakaiki hospital jikinki yafara zafi”. Kama hanunta yay oya muje kisa kaya tana manne dashi sukaje daki doguwar riga ya ciro mata ta karba ta shiga bayi tasa tafito yay murmushi baice mata komiba, ya dauko mata shawarman taci agabanshi, yabata paracetamol, tasha sanan yace ta kwanta ta shagwabe” a falo zan kwanta zan kalli series ne “Love is timeless ” to muje yadau filo da blanket ya kwantar da ita ya lullubeta da blanket ya kunna mata kallon sanan yamata kiss a goshi yadau briefcase dinshi yafita. Murmushi tayi tace “luv u too” sanan ta gyara kwanciya tacigaba da kallon ba dadewa bacci mai nauyin gaske yay gaba da ita. Tic-tic-tic-gilin agogon garin Abuja ya nuna 11:00Am na safiya. Zaune mai gadi yake yana jin sakon gaisuwan radio yaji anama gate bugun hauka, da sauri ya tashi yabude dan karamin marfi ya hango wata yar tsohuwa,baka, zani daban riga daban sai irin dankwalin da dinan ga wani uban goro a hanunta tana gutsura. jin takara bugawa yasa yace “wonene? Cikin hausar shi mara kyau “Nice dan uwarka wurin jikata nazo” mai gadi bai bude ba dan atunanin shi mahaukaciya ce. Securities dake hanyar shiga part dinsu Barraq Su biyu da kakin sojoji ajikin su yaje wurinsu yace “mahaukaciya kuzo ku koreta” daya daga security yabi bayan mai gadi bude gate yayi tsohuwar ta shigo da sauri ciki security yace” Hj nan ne gidan Barrister Barraq,nuna mana ID card dinki?” Tsohuwar tace” kaci ubanka menene kuma idi ked?” ta balli goro kafin tace” ka matsa na shiga wurin yata”, Dadai security yaga kaman ahaukaciyar ce yasa ya sassauta murya “Mama ba’a shiga gidan Barrister idan baka da ID card,kokuma bakada appointment dashi for security purpose, mussamman gwamnati ta nadamu, aikin mune kula dashi da iyalenshi,Babban Barrister ne a Abuja,saboda tsaro, bamusan kiba dan Allah kiwuce kifita kafin mu koraki mama” tsohuwar ta zaro ido “yanzu nida gidan jikata zaku koreni?,Ah lalle, ke duniya mekika zama??nazo ganin jikata ne, kuma nan ne gidan nasani,shine zaku koreni??” ta tsugunna a wurin ta fashe da kuka security ya tsugunna “mama kodai kin batane?” cikin kuka tace” wlh nanne,nanne gidan” tadanyi shiru tana kokarin tuno yanda aka koya mata maganan da zatama security tasake cewa” nine kakar Rufaida matar Barraq din,bakistan dakake fada ai suruki nane, Duduwa ce fa,kakarta ce, koku bani hanya nawuce ciki konasa Barraq ya koreku inya dawo wlh. Sainasa kun rasa aikin ku shegu masu kama da samudawa,ga shegen girma, ga bakin fata, ga fuska ba rahama,Ga uban muni kaman kacin wanda yasha zobo
Title :
Kaine Sirri Na Part 20
Description : Da sauri ta tashi ta rungume Hafsat tana mai tsanin farin ciki. Hafsat ta dagota da sauri”Anty Rufaida jikin ki zafi sosai, baki da lafiya ...
Rating :
5