Wuraren karfe 11:30 na dare ya dawo, Solomon yakira ya kwaso mishi kayan cikin motan,katon ganamasgo ne wanda naira miliyan 2 ke ciki,wanda gwamnati yabata sai katoton akwati daya biya super market yayo mata shopping kaya nasawa da dama dakuma hijabai manya tunda ya lura ita ustaziya ce, saikuma dan kayan ciye ciye daya siyo mata,murna sosai yake dan gobe bayan yadawo daga Court zai koma Abuja, visa zai mata yakaita Russia wurin Mum,tana mugun son yara,shikadai ta haifa dan yama sanar da ita yasamo mata yarinya,iyayenta sun mutu,mamarshi tanata murna zata samu yarda zata kula da ita. zai kaita wurin Mum tai makaranta a wurin.. maganan Solomon ya katse mai tunani “sir dakinka zankai kayan kona madam?”da murmushi akan fuskanshi yace “shigar dasu dakinta ka ajiye, idan nai wanka zan shiga wurin”, ya wuce dakinshi yayinda shi Solomon ya bude dakinta ya ajiye kayan a gefen gado bai damu da rashin ganinta ba dan yazaci tana bandaki ne yafito ya mayar da kofan yarufe yatafi wurin kwananshi.
Bayan ya gama wanka,ya sanya pyjamas din bacci ya kalli agogo lokacin yaja dare yariga yaraba, dan alokacin 12 na dare yadan gota, tunanin dayayi nacewa yanzu haka tadade dayin bacci yasa kawai yaja bargo yay baccinshi gobe da safe kafin sutafi Abuja yamata bayani.
Karfe hudu na asuba tai musu a tashan garin Jigawa,sauka tayi sukai sallama da matan,tace” to Rufaida Allah Kara hada fuskokin mu,mijina yazo daukana”ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsa “to Mama Allah kaiki lpy,agaida yara”. Tasamu tadan zauna akan wani kujera da aka tanadarma masu tafiya bacci yadan dibeta sai Wuraren 5 na safiya sanan ta tashi taje jikin wani dan masallaci dataga mutane ta dibi ruwa tai alwala sanan takoma Chan gefe guda tai sallolin da ake binta,sanan tai ra’atanil fajir saitai sallan asuba.
Karfe shida ta shiga motan dazaikaita kauyen GUJUNGU itakadai ne aciki ta biya dari biyu kudin mota. tai shiru kaman marainiya tana kallon mutanen wurin dasuke Shan koko da kosai,kaman taje ta roka saboda yunwar dake cin cikinta hakanan ta daure sai Wuraren 8:30 motar ya cika sukadau hanyar kauyen gujungu.
Bayan yagama al’adunshi na safe,ya fito cikin 3quater dayar short sleeve dinshi fara fat yana rike da karamin kofin coffee ya tura kofan dakinta ya shiga,ganin bai gantaba yasa yakoma kan kujera yay crossing legs yana Shan cofee a nishadan ce, yadau remote ya kunna TV bango,atunaninshi tana bayi, ajiye cup din coffee yayi akan stool din gefen kujeran ya kalli agogon hanunshi almost 15 min da shigowan shi batafito daga bayi ba kuma baimaji alamun saukan ruwa a bayin ba. Tashi yayi da sauri ya tsaya a gaban kofan bayin ya kwankwasa ” Hi sister kina ciki?” Yaji shiru da sauri ya bude bayin yaga babu kowa aciki, a rude yasaki kofan bayin ya juyo sai alokacin idonunshi suka sauka kan wallet dinshi daya gani a bude wasu ID dinshima akasa sun zube karasawa yayi yadaga ya mammaida ya kulle sanan ya fita zuwa kasa dakinsu Johnson ya tambaye su kunga yarinya na? Kowa yace a’a,yace “Solomon jiya dakaje ajiye kayan nan baka ganta acikiba?” Yace “no sir,babu ita I thought tana bayi saisa ina ajiyewa na fito na kulle kofan”, Barr yace”God! I pray yarinyar nan ba guduwa tayiba” yakarasa wurin securities masu tsoron gate ya tambayesu wanda ke duty jiya yace “Sir jiya duk Wanda suka shigo hotel dinan dawayan da suka fita babu wacce tasa hijabi,sai wata yarinya black beauty haka sir,batada kiba sosai, kuma batada tsawo sosai,quite sure naga daga part dinka tafito da gudu,she was crying self lokacin datafita”.
Barr Barraq yace” damn it,wot is your problem mandawari?,kaga karaman yarinya tafito daga part dina tana kuka baka tsayar da itaba”,yakara dakamai tsawa “Kaine a duty ranan Dana kawo yarinyar nan wurin nan,u saw lokacin dasu Johnson ke shigar da ita ciki,but duda haka u let her go”, mandawari jikinshi na rawa yace “sorry sir,a gafarceni,wlh ranan ba kalli fuskanta da kyau bane” ya kalleshi da jajayen idonshi yace “u no nothing akan job dinka,so just pack ur things nd go, nakore ka” yajuya yakoma ciki Johnson da Solomon suka rufamai baya,mandawari yafashe da kuka ya zube akasa “dan Allah kayakuri sir,wlh bazan Kara kuskure hakaba” ko juyowa baiyiba daki yakoma ya dauko car keys,ya fito ya shiga yaja motan da bala’in gudu yana zukan taba yabar hotel din.
A daidai kauyen gujungu aka sauketa,ta sauka tana tunanin uban tafiyan dazatayi kafin takai cikin kauyen, a hankali take daga kafa take tafiya tana Kara kallon kauyen rabonta da kauyen kusan wata shidda kenan, cikin sa’a taga mai amalan ken data Sani abokin Abba ta tsayar “Baba ina wuni” tafada tana murmushi Kara kallonta yayi yana goge idanu “wanake gani? Rufaidatu ce?” “Eh Baba nine”, ya sauri yace” a hayo, hayo mana, hannu Rufaidatu” tahau kan amalan ke,ya shau dama jakunan bulala suka fara tafiya, sanan yace”Rufaida ya hakuri? munji Malam Musa,da Asiya sun rasu daga bakin Duduwa,dan hargarin nan wasu polisawa sukazo ana nemanki,aka kuma sanar damu rasuwan iyayenki ta hanyar rushewan gini”. Hawaye ya cika mata ido “Alhamdulillah Baba” yace” Amma Rufaida maiyasa ki kara dawowa kinsan yanda Duduwa ta tsaneki,duk yanadaga cikin abunda yasa Musa marigayi ya Tattraku yabar kauyen daku saboda jaraban mahaifiyar shi Duduwa” cikin kuka tace “Baba banda kowa, sai Duduwan dole na dawo koda kasheni zatayi”, girgiza kanshi yayi yace”hakane Rufaida karki damu Allah natare dake,ki dage da addu’a Allah ya dauraki akanta ” tace” to Baba nagode”.
Haka suka dinga fira sama sama harsuka shigo cikin kauyen. Kauyene sosai, ko ina yara da yanmata anci atampa daban riga daban dan kwali daban ga dige dige a fuskannan sai kallonta suke dan basu ganetaba tasha hijabi abinda basu saba ganin yan matan garin na sawaba, a kofar gidan Duduwa ya sauke ta, ta sauka amma tasami kanta da kasa shiga gidan saboda tsoron Duduwa, kuka tafashe dashi sosai tana yarfe hannu, Baba ya tausaya mata yace” Rufaida ki shiga da bissmillah Allah na tare dake kinji yata karkiji tsoro” ta goge Hawayen wasu na zubowa tace “to Baba nagode”
Bude buhu kofar gidan tayi ta shiga ahankali tana tafiya a zauren, kunenta suka juyo muryan Duduwa na rera waka”Ladi mai kidan kwarya aja kida asha dadi …ari, kai anata sabon daa wayake ta tsohon da.. Ari, saidai munafukai su kalleni Niko ai inada nerori ..Ari, Alhakumu aljanna kubari infadi da hillanci.. Ari”
Hawayen idonta ta share, jikinta na rawa, ahankali ta rera sallama “Assalamu alaykum