Da sauri Rufaida ta sakko daga gado tana kuka sosai, tazo kusa dashi ta tsugunna tana kallon yanda yake cije lebe muryarta na rawa tace “Uncle B menene? ” da kyar yabude ido ya kalleta ya mata murmuahin dole yace “am fine baby, jekiyi bacci”kuka tafashemai dashi tana girgizamai kai. Jawo hanunta yay ya kwantar da ita a gefenshi yana share mata hawaye kafin yatashi da sauri yaje wurin jakarshi yabude yadau kwalin taba da lighter yafita daga dakin, kasa ya sauka Ya zauna a falo yazaro kara biyu yafara zukarsu atare da sauri har tari yake kaman mahaukaci Saida yasha kusan 5 sanan yaji daiddai yay bacci awurin.
Wuraren 5:00 na asuba yabude ido ganin Rufaida zaune agabanshi kanta akan kujeran dayake kwance tana bacci hawaye a gefen idonta yasa yaji wani irin sonta da tausayinta, hanunshi ya daura akanta ahankali yace”Allah yay miki albarka matata” tashi zaune yay ya dauketa yakaita daki,ya shimfideta kafin yaje bayi brush da alwala yafito Ya zira jallabiya,saida yakara dawowa gaban gadon ya kalleta ya sumbaci goshinta kafin yafita zuwa masallaci.
Baidade dafita ba tatashi ta shiga bayi tai wanka tareda dauro alwala tazo tai sallah. Bayan ta idar ta linke dadduman, tunawa da abinda Mum tafada mata yasa ta dauko riga da sket daga akwatinta pink tasaka, rigar ta matseta ga wuyan rigar V neck gareta hakanan tasa saboda duk sauran kayan English wears ne. hakama sket din ya kamata. tana gamawa tai kwalliya ba sosai ba amma tai kyau barin gashin kanta tayi abude. Ta gyara dakin koina. ganin 6:30 tayi ta sakko tana neman kitchen. Shiga kitchen din tayi ta gyara kafin tafara dafa ruwan zafi ta juye a flask, ta soya plantain da egg duk takai dining ta jera tadawo tai toasting bread tadai hada komi ta kara gyara kitchen din. Da sauri takoma daki tabude akwati taciro turaren wutar da Mum tabata ta kunna,ko ina yadau kamshi sai murmushi take tunawa datayi yanzu fa tanada lada takoma daki ta tafesa turarukan da Mum tabata sanan ta dauko Biology note dinta tafito tadawo kasa ta zauna akan doguear kujera tana karantawa. dukta gaji da zama ita daya, kukan tsuntsaye kawai akeji,ba motsin kowa,tsoro ma yacigaba da kamata. Wuraren 8 Ya shigo gidan da sallama kanta akasa ta amsamai, yana karasowa cikin falon ta zamo daga kan kujera ta tsugunna tareda furta “ina kwana “murmuahin jin dadi yay yakarasa gabanta, yasa hannunshi biyu ya dagota ya rungumeta “Hey Baby na,kidena tsugunna wa inzaki gaidani” yakara matseta ajikinshi yana jin dadin kamshi dake tashi ajikinta,”inasonki sosai” lamo tayi ajikinshi murya chan kasa tace”namaka breakfast “cikeda murna ya dago da kanta yana murmushi,komar da gashin dake neman sshigan mata ido yay gefe ahankali yadan rage tsawo ya sumbaci goshinta da sauri ta lumshe ido “thank you Baby na,kayannan sun karbeki” tadanyi murmushi jin dadi, yace”naje nai wanka kafin nazo naci?” Yatambayeta yana kallon fuskarta kanta akasa tace “eh” kiss yamata agoshi kafin ya zaunar da ita yatafi sama donyi wankar. Kusan minti talatin ya dauka sanan ya sauko kasa sanye da suit baki,sai kamshi yake zubawa,ahankali ya karaso gaban kujerar datake,ya mika mata farin hanunshi alamun ta tashi,kasa mika mishi nata tayi ta kara dukar da kanta kasa, murmushi yadanyi kafin ya kama hanunta ya dagata, sai wani noke kai take ahaka har sukakai dining sakin hanunta yay yaja kujera ya zauna yana kallonta,saida tadan saci kallonshi da sauri ta dauke kai ganin ita yake kallo,tadau plate tai serving dinshi ta hadamai tea a cup sai binta da kallo yake yanda take komi a natse,bayan takai komi gabanshi tajuya harda saurinta zatabar dining taji ya damko hanunta, ahankali ya janyota ya daurata akan cinyarshi hakan yasa wani irin kunya yakamata ta kulle ido tana kokarin boye fuskarta, fork ya dauka ya dauko plantain daya dashi yakai saitin bakinta “open ur mouth ” kara juyar da kanta tayi tana kokarin tashi daga jikinshi, “open baby ” da kyar ta juyo mai da kanta ta bude bakin ahankali ya sakamata ta gutsiri kadan taci, yacinye saura yana karemta kallo yanda taki bude ido. Haka yaacigaba da bata har suka cinye. Karan wayarshi dasukaji yasa yace “daukomin wayana,yana bedroom” ahankali ta bude ido ta saukesu akan fuskarshi, ta mike zata tashi ya fizgota takara fadowa jikinshi, da sauri ta tashi da gudu tahau bene ta shiga dakin tana haki daukar wayar dake ringing akan gado tayi tajuya tasa hannu zata bude kofar kenan ya shigo yana mata murmushi da sauri taja baya. Maman Abd Shakur
Tanaja baya yana binta harsukakai jikin bango ahankali yariketa yace “wana kama?” Murya Chan ciki tace ” am thorry” hanunta yaja ya zauna abakin gado ya daurata akan cinyarshi kafin yace “who called? “Mikamai wayar tayi ya karba ya duba muzammil ne,yadafe kai yace “O,nama manta”,Ya kalleta “u see kinsa namanta da kowa” kokarin kiran layin Muzammil yay yaji busy, dan tsaki yadanyi “who are u talking to again”…bai gama maganan ba yaga kiran Muzammil ya shigo da sauri ya dauka “am sorry mana,ganinan zuwa, just make sure u close her mouth, I’ll be there in a minute “. Ya katse wayan tareda kallon Rufaida daya lura tunda yafara wayan take kallonshi. sa hannu yay yadaga fuskarta tadan kalleshi “am going out,ki kula da kanki kinji baby na, mezan siyo miki?” Gizgimai kai tayi, zaunar da ita agefen gado yayi yatashi yadau wata yar jaka yarike kafin ya dawo wurin yamata kissa agoshi “I luv yhu, bye”. Hawaye yacika idonta sosai, yajuya zai fita yaji tafashe da kuka da sauri yajuyo “Baby menene kike kuka?” Kai ta girgiza mai “am scared, banason zama nikadai,tsoro nakeji” masauki yamata a kirjinshi ya daura kanshi akan nata ya lumshe ido, yana shafa bayanta “don’t worry,babu abunda zai kamaki,kinji . inkira miki auta ta zauna dake kafin nadawo?” Da sauri ta dagamai kai, hannu yasa yashare hawayen idonta “ok to dena kukan” zama yay akan gado ya daurata ajikinshi kafin ya ciro wayar shi yabata “tayani dailing number Amma” saida tadan kalleshi kafin ta karba ta nemo number daga contact dinshi tai dailing tabashi, kanta akasa karba yay da hannu daya yakara a kunne cikin girmamawa ya gaida Amma yamata bayanin yanason Auta tazo anjima zai dawo da ita, Amma tace to barita shirya direba yakawota, Barraq yace to tareda mata godiya, kafin yakira direban gidansu yaymai kwatancen gidan sanan ya ajiye wayan yana kallon Rufaida dayaga tana wasa da yatsunta. Kama yatsun yayi yajuyo da ita yasa hannu ya daga kanta, dan murmushi tayi dimple dinta suka lotsa, Barraq ya hada kanshi da nata “Rufaida!” Ta dago ido ta kalleshi “I luv yhu sosai” lumshe ido tasakeyi,tareda sakin tattausan murmushin dake kashema Barraq jiki. “Duk randa narasa ki,ranan na tabbatar zan rasa raina,zan shiga mawuyancin hali, kona haukace ma,bansan mesa nake sonki ba, kawai all I know is I luv yhu darling, u are special ” zamewa tayi daga jikinshi taruga da gudu zata shiga bathroom dan wani irin kunyan magananshi takeji yarike hanunta,yakara jawota yahada hannayensu akan cikinta ya lumshe ido, itama ta lumshe ido “ninasan danni aka yiki, bantabajin son wataba sai ke my pretty angel,zamu gina soyayya mai karfi,na amana da kauna, zaki haifamin plenty babies ko?” Fizge jikinta tayi tafada kan gado taja bargo tarufe fuskarta tana murmushi ahankali, maganarshi kunya yake bata, Barraq yazo kusa da ita akan gadon yakara bakinshi a kunenta yana murmushi yace “Inason kunyarki,everything fits yhu,everything namiki kyau”daga kanta tayi ta chusa hannu akunnen ta tana jujjuya kanta cikin yar karamar muryar ta tace “Uncle B plz stop,kunya nakeji” jawota yay kan jikinshi yana murmushi,”to bari nakori kunyar” ahankali yakai hannu kan zip din bayan rigarta ya zuge,yafara wassanni da ita na fitan hankali. Ina ganin haka nafito daga dakin. Direba ne ya sauke Auta a haraban gidansu,da gudu ta diro tun a tsakar gida take kwalamai kira “Uncle B,Uncle B, i missed yhu”,falo ta shiga tafara waige waige tana kwallamai kira, tahau bene da gudu tai sama da kyar Barr ya iya sakin Rufaida dakemai kuka tana kakkare kirjinta,murmushi yay ya lashe lips dinta yace”get dress and come downstairs ga auta hartazo” yamike yana gyaggyara suit din jikinshi sanan yafita daga daki, cin karo yay da Auta tana waige waige wani ihu tayi ta dane jikinshi “Uncle B oyoyo” shallata sama yayi yana murna,, sanan ya ijiyeta akasa da sauri tafara waige waige “uncle ina Anty Rufaida baka tahomin da itaba? Amma fa tacemin tare kukazo”. ta marairaice tanason tai kuka. Hanunta yakama suka fara sauka daga kan stairs yace” gatanan zuwa,tana dan aiki ne ” chak auta ta tsaya ta kalleshi yace”wot again?” Ta marairaice tace “nidai ka goyani nagaji da tafita akan bene”, Barraq ya rike harbarshi yace”shows! Wai bakisan kin girma ba yanzu?”kuka tafaramai “wlh ni har yanzu am Auta 11 and half nefa shekaruna, ni dai ka goyani, kaga kai kadaine yayana ai kadinga jidani,hakama Anty rufaida zata dingamin”. Kada kai yayi ya tsugunna ta dane bayanshi da gudu yatashi sanan suka karaso kasa ya sauketa duk suka zauna. Kayan jikinta takarasa cirewa tadau wani pink fitted doguwan riga na cotton yakamata sosai yafito da shape dinta,gyalenshi ta yane kanta dashi tadau turare tafesa fuskarta ba kwalliya amma tai kyau, kayan sun mugun amsanta, ahankali tasa hannu ta bude kofa tafito tana tafiyanta a natse mai daukar hankali. Kamshin daya bugi hancin Barraq da Auta dake zaune suna hira yasa suka dago kai, Barraq mutuwar zaune yay Auta ta tashi tsaye da sauri tana ware idanu tace “wow! Anty kinyi kyau” daidai nan Rufaida takaraso kasa tasakarma Auta murmushi cikin muryarta mai Sanyi tacema Auta “nibaza kimin oyoyo ba?” ta budema Auta hannu da gudu Auta tafada jikinta ta rungume hartana neman fadar da Rufaida. Barraq dai yana zaune yana murmushi,Rufaida takama hanun Auta suka zauna kan kujeran dake nesa da Barraq suna hira,auta tace” Anty Amma tace nakawo miki wanan ” da gudu Auta ta dauko Jakarta tabama Rufaida dambun naman kaza dayawa, Rufaida tai murmushi jin dadi takarba. Barraq dai dayaga ko kallonshi basayi Auta sai dariya takesa Rufaida yasa yakoma yadauko jakar da keys din motarshi yafito, Ya kallesu yace”natafi anjima kadan zan dawo,Rufaida kanta nakasa dan mugun jin kunyar kallonshi take saboda yanda yay wasa da jikinta dazu kanta nakasa tace “saika dawo,Allah kareka” Autama tamishi saiya dawo. Ameen ya amsa musu yafita suka cigaba da hira,tana jin dadin yanda Auta kebata labarai kala-kala. Maman Abd Shakur
Banban wajene katoto babu komi awurin sai goods dake cikin manya manyan kwalaye. Nana nagani akan kujera tana sanye da kayan banzan data saba sawa an daure kakafunta da hannayenta an rufe bakinta da salataf sai mutsu mutsu take alamun tanason tai magana. Muzammil dake zaune kan kujera yataso yazo gabanta ya tumbuke salataf din da karfi Nana tai ihu “auch Muzammil bazakamin ahankali ba,matsalan mutum talaka fa kenan, shege boyi boyin Barraq,yaga saurayina maikudi jinin yan Russia, wlh dazaran ya aureni zanrabaku.” Muzammil bai ce komiba illa cewa dayayi “mekikeso kiketa mutsu mutsu?” Nana tamai wani fari da ido Tace” sonake ka Kwance ni, natafi kafin B yazo,nai alkawari zan shayar dakai xuman dabaka tabashan irinshi ba wlh”. Muzammil yay tsaki “yhu are damn crazy Nana,bana neman HIV, karki damu lokacin danakeso yashige ni zan nemoki ki samin” zatai magana yadau salataf zai manne bakin kenan Barraq ya shigo. bude ido Nana tayi tana kallon Barraq yanda yay kyau yakara haske gashin kanshi yakara yawa da cika kaman wani balarabe. rungume juna sukayi shida muzammil Nana ta runtse ido” B dan girman Allah ka rungume ni, maisa nakeson haka B, wlh I will kill dat ur mumu wife,wanan yar kauyen,shegiya mai kama mayu, B maizakayi da yarinya yar kauye dabazata wuce 16 years ba,gani jibenifa”,tadan jijjiha jikinta “me tafini? Wayewa? Hasken fata? Ilimi ko diri”? Kaman zararriya tai ihu “I just can get it why did yhu hate me Barraq? Bayan kasan dani kadai zaka iya more rayuwar aure?” Barraq baice mata komiba saima cigaba da maganan da yakeyi da muzammil yayi. da karfi Nana tace “Barraq! Yajuyo ya kalleta” wlh ,wlh inhar baka auran ba bazaka taba samun zaman lpy da matarka ba, saina addabeku, saina kashe matarka, nakashe ka,sanan nakashe kaina. I luv yhu alot”.
tafashe da kuka. Sai alokacin Barraq yay magana yace “u don’t luv me,wot u feel is not luv Nana is Obsession! Idan kinasona bazakizo ki cutar daniba”. Nana taware ido “wlh bazan taba cutar dakaiba in my life, I swear by Allah” Barraq yay murmushi yabude yar jakan hanunshi yaciro chocolate din da Nana tabashi har Rufaida taci rabi tabar sauran, tundaga lokacin yake preserving chocolate din afirij babu abunda yayi saidan chabewa dayayi yace “mekikayi niyyan yimin da abunan?” Nana ta zaro ido tana kame kame ya daka mata tsawa “mekikasa a chocolate dinan?” Tai shiru batace komiba. “Matata taci abinan, she suffered, alkawari daya na daukarma kaina duk Wanda ya wahalar da matata saina rama mata, nasa ankamoki ne only dannasaki kema kici chocolate dinan,I want yhu to feel wot she felt alokacin”. Nana ta zaro ido “plz karkai haka B,forgive me, karkaban, sonka ne yaja naihaka”. Barraq yakarasa gabanta da sauri Nana tace “wait, inhar kamin haka wlh sainaje na dauko kakar matarka daga kauye DUDUWA! kasan duk duniya babu wacce matarka ke tsoro kaman DUDUWA, Barraq am warning yhu don’t mess with me,yhu have no idea wot am capable of” . Barraq ya kalleta “waye baki information akan my family and everything about me? Ya akayi kikasan DUDUWA? Yama akayi ranan kikasan zanje Russia? harkika saman a airport, I know is not co incident, I don’t believe in co incident, tell me” Nana tai murmushi tana kadamai idanu “I will only tell yhu if u spend a nyt with me Barraq, just one nyt.
Idanun Barraq sukai ja,”stay away from me and my family Nana, nafada miki be very careful. Karki tabamin Rufaida cuz I can do anything akan Rufaida, I mean anything!” Nana tai ihu “stop calling her name, I hate her! wlh sainasa an farke shegiyar” Barraq ya falla mata mugun mari saida bakinta yafashe, zai karamata wani Muzammil ya rikeshi Ya girgizamai kai, Barraq yasa hannu ya matse bakinta Ya chusa chocolate din ciki ya rike hancinta ba shiri Nana tahadiye tana ihu “wlh saina kasheta, u will see” warwareta muzammil yayi yarufe bakinta da salataf ya jefata a boot din motarshi yaja motar har kofar gidansu Nana, bakowa a anguwar, ya bude boot yaga idanun nana sun chanza, rumgumeshi tayi da sauri ya hankadata ya cizge salataf din bakinta,yabude gate ya wurgata cikin gidansu ya koma motar shi yaja da sauri yabar kofar gidan.
Maman Abd Shakur.