Zaune yake a wani babban wurin hutawa dake gidansa. Wanda dama an ware gurin ne domin hutawa na lokaci zuwa lokaci.yar bukka ce gwanin sha awa irin ta turawa.gurin shirye yake da kujeru na hutawa sannan kuma fulawoyi iri da kala wasu har tukunya.kallo daya zakayi wa gurin ya nishadantar dakai.domin gurun ya tsaru dole yayi dadin hutawa.kallo daya zakayi masa kasan yana cikin damuwa.jigum yayi yana nazari cikin zuciyarsa.yarasa yadda zaiyi ya fitar da tunaninta a ransa duk da kuwa yasan abin bamai yiwuwa bane.takaicinsa daya shine baisan inda zai ganta ba idan yatashi nemanta.a koda yaushe da wannan tunanin yake kwana kuma dashi yake tashi.saukinsa daya shine idan ya kalli kyakkyawan fuskarta da ke dauke da murmushi a jikin screen din I-pad dinta.sallama tayi takai yakai kusan sau uku.firgigt yayi ya cira kai yadubeta.sister dinsa ce amal.sannan ya dauke kai bayan ya amsa sallamarta.guri tasamu tazauna yadda zataji dadin fuskantar same.murmushi tayi sannan tace yaya ahmad barka da hutawa.ya maganar fitar? ko kun fasa be? inata magana bakaji ba. ko tunanin anti no name kakeyi? pls yaya ahmad ka fitar da wannan tunanin kadawo normal person kamar da.sam ni yanzu banaji dadin komai. tun faruwar wannan al'amarin nadaina samun kulawarka ya Ahmad.ka manta da duk abubuwan da kayi asara a naka I-Pad din kanata tunanin abunda baka sani ba ita din ko matar aure ce.kadaure kayi hakuri don samun saukin damuwarka ka fauwalawa Allah.sam ni yanzu kasa fara jin haushinta saboda tasa nadaina ganin farin ciki sosai a fuskar ka.pls ya ahmad ka saki ranka.na fuskanta ko ta auntyna anisa bakayi sai nata!".kuramata ido yayi cikin damuwa dakuma jin haushin furucinta.yace amal kibar gurinnan idan bawai zuwa min kikayi da magana mai dadi ba.
Title :
Jinin sarauta part 1
Description : Zaune yake a wani babban wurin hutawa dake gidansa. Wanda dama an ware gurin ne domin hutawa na lokaci zuwa lokaci.yar bukka ce gwanin sha a...
Rating :
5