" Mafiyawancin Malamai dake sukar lamirin samar da Film village da gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar samarwa a birnin Kano, babu adalci da adala a cikin dukkanin maganganun su, kuma suna yine da wata manufa amma ba domin taimakon addini da al'ummar musulmai ba".
Wannan kalami ya fito ne daga bakin wani tsohon janar mai ritaya mai suna janar Kabir Galadanchi, a lokacin da yake ganawa da manema labarai a farfajiyar gidanshi dake unguwar Barakallahu kaduna.
Janar Galadanci ya ci gaba da cewar, harkar fina-finan Hausa, harka ce ta ci gaba kuma wacce take taimakon al'ummar Hausawa da al'adunsu, sannan take samar da ayyuka ga matasanmu, saboda haka abune wanda ya dace malamai da shugabanni su goyi bayan shi, kuma su shigo ciki domin bada tasu gudummuwar, saboda cigaba da aka samu na zamani.
Janar din ya bada misali da wani Fim da akayi shekarun baya cikin harshen turanci na tarihin Annabi Muhammadu SAW mai suna "The Message" inda yace ba musulmai bane suka shirya wannan fim din, amma sai gashi ya amfani dukkanin musulmai a fadin duniya, to me zai hana mu bada tamu gudummuwar ga 'yan uwanmu musulmai domin suma su cigaba da gudanar da harkar fim saboda cigaban rayuwarmu.
Janar Galadanci ya bada tabbacin inganta harabar gidanshi domin mayar dashi fim Village, da mika shi ga jaruman fim din Hausa domin horas da 'yan wasan fim maza da mata saboda inganta rayuwar matasan hausa, domin babu wani Malami ko wani Sarki ko wani dan kasuwa a Arewa wanda ba'a kallon fim din Hausa a gidanshi.
Rariya
Title :
Janar Kabir Galadanci Zai Gina Fim Village A Jihar Kaduna
Description : " Mafiyawancin Malamai dake sukar lamirin samar da Film village da gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar samarwa a birnin Kano, babu ...
Rating :
5