Jagoran addinin Iran din, Ayatullahi Khamenei ya bayyana gidan sarautar Sa'udiyyar a matsayin mugaye kuma la'anannu.
Ya kara da cewa ce gidan sarautar Sa'udiyyar ba su cancanci su zama wadanda wurare masu tsarki na Makkah da Madina ke karkashin kulawarsu ba.
Jagoran addinin Iran din ya shaida wa wadanda 'yan'uwansu suka rasu a turmutsutsin hajjin bara cewa sakacin hukumomin Sa'udiyyar ne sanadiyar mutuwarsu.
Related News: Yan Iran Ba Musulmai Bane - Saudiyya
Shi ma shugaban Iran din Hasan Rauhani ya yi tir da Sa'udiyyar a taron majalisarsa ta zartarwa, inda ya ce wajibi ne a dora alhakin lamarin a kan gwamnatin Sa'udiyyar.
Koda ministan harkokin wajen Iran Muhammad Javad Zarif ya ce, hakika akwai bambanci tsakanin musulunci da wahabiyanci da irin tsaurin ra'ayin da Saudiyya take yadawa a duniya.
Tuni dai Amurka ta tsoma baki cikin wannan lamari inda ta ce, musayar kalaman masu zafi tsakanin Saudiyya da Iran zai kara ruruta rikici ne a yankin gabas ta tsakiya.
Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce, ba ta ji dadin yadda kasashen biyu suke musayar kalamai masu zafi ba a tsakaninsu.
Cacar bakin dai ta samo asali ne yayin da Iran ta zargi sarakunan Saudiyya da gazawa wajen gudanar da aikin Hajji.
Iran ta fadi hakan ne dangane da turmutsutsun da ya kai ga mutuwar alhazai fiye da 2000 bara, kuma 400 daga cikinsu 'yan kasar Iran ne.
Source Bbchausa
Title :
Iran Ta La'anci Sarakunan Saudiyya
Description : Jagoran addinin Iran din, Ayatullahi Khamenei ya bayyana gidan sarautar Sa'udiyyar a matsayin mugaye kuma la'anannu. Ya kara da cew...
Rating :
5