Kungiyar Boko Haram bangaren da Abubakar Shekau ke jagoranta, ta watsa sabon faifan bidiyo, wanda a ciki Shekau ya musanta kirarin da rundunar sojin Najeriya ta yi na cewa ta raunata shi a wani hari da ta kaiwa maboyarsa watan da ya gabata.
Cikin bidiyon da kungiyar ta watsa a shafin Youtube Shekau wanda yayi Magana cikin harsunan Hausa, Kanuri da kuma Larabci ya bayyana cewa yana nan garau babu abin da ya same shi.
A watan Augusta rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa Shekau ya samu mummunan rauni a farmakin sama da ta kai maboyarsa, wanda kwamandojin kungiyar ta Boko Haram da dama suka rasa rayukansu.
Har yanzu dai rundunar sojin najeriya bata maida martini ba kan sabon bidiyon.