Assalamu alaikum Allah shi gafarta Malam. Shin menene hukuncin irin rantsuwar nan da mutane sukeyi da Alqur'ani ?.
Kamar a Kotuna sukan sanya mutum yayi Alwala sannan yazo ya dafa Alqur'ani yayi rantsuwa akan wani abu. Shin dole ne sai mutum ya dafa Alqur'anin? Kuma shin idan bai cika rantsuwar da yayi ba, akwai kaffara akansa?
Sannan mutane koda acikin zantukansu na yau da kullum zaka ji suna yin rantsuwa da Alqur'ani. Shin Yaya matsayin wannan yake?
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Shi Alqur'ani zancen Allah ne, Shi kuwa zance yana daga cikin siffofin Allah (SWT). Don haka ya halatta ayi rantsuwa dashi. Ko an ta'bashi ko ba'a ta'bashi ba.
Imamu Malik da Shafi'iy da Imamu Ahmad dukkansu sun ce rantsuwar ta yiwu.
Awajensu sun ce idan mutum yayi rantsuwa da Alqur'ani cewa sai yayi abu kaza, to idan bai yi abinda ya fada dinba, sai lallai sai yayi Kaffarah.
Ibnu Abdil-Barri acikin littafinsa AT-TAMHEED ya kawo zantukan Sahabbai da tabi'ai game da Wajibcin yin kaffarar.
Akan adadin kaffarar da mutum zai yi kuwa, Imamu Abu Haneefah da Imamu Ahmad sun ce sai yayi ma kowacce ayah guda nata kaffarar dabam. Amma Imamu Malik da shafi'iy sun ce idan yayi kaffarar guda daya ma shikenan.
Rantsuwar da mutane suka saba yi acikin zantukansu wannan ba za'a dauketa amatsayin cikakkiyar rantsuwa ba.
WALLAHU A'ALAM.
(20-08-2018. 17-11-1437).
ZAUREN FIQHU
Title :
Hukuncin Wanda Yayi Rantsuwa Da Alqur’ani Mai Girma
Description : Assalamu alaikum Allah shi gafarta Malam. Shin menene hukuncin irin rantsuwar nan da mutane sukeyi da Alqur'ani ?. Kamar a Kotuna suka...
Rating :
5