Gwamnatin Najeriya tayi watsi da shawarar tsoffin shugabanin kamfanin man kasar na kara farashin man saboda abinda suka kira hauhawar farashin dala da ake sayo man da su.
.
Hukumar kayade farashin man tace gwamnati bata da niyyar amincewa da wanna bukata saboda ganin halin da talakan Najeriya ke ciki.
.
Tsoffin ma'aikatan sun bukaci gwamnati da ta sauya batun kayade firashin man domin baiwa kowani dan kasuwa daman siyar da shi yadda ya kama, batun da babu shaka zai haifar da tashin man.
.
Al'ummar Najeriya dai na ci gaba da kokawa da matsayin firashin mai a kasar wanda ke sake jefa talaka a cikin hali na kunci.
.