Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta samu nasarar kama wani kwararren mai hada wa kungiyar Boko Haram bama-bamai mai suna Idris Audu a lokacin da yake kokarin shiga aikin soja a Kano.
A cikin wata sanarwa, da hukumar ta DSS ta fitar ta ce, an kama mutumin ne sakamakon wani aikin hadin gwiwa tsakanin jami’anta da na rundunar sojin.
Lamarin dai ya zo ne bayan samun bayanan sirri da ke cewa mayakan kungiyar na sake tattaruwa a birnin Kano.