Kwamishinan lafiya na jihar Filato Dakta Kuden Kamshak ya sanar da sake bullar cutar zazzabin Lassa a jihar Filato, yayin da aka tabbatar da ta kama wasu mutane 2 da suka hada da wani dalibin jami'ar Jos da kuma wata Bafulatana.
A yayin wani taron manema labarai da aka saba gudanar wa kowanne satin farko na wata, Kwamishinan ya bayyana cewa, tuni an yi wa dalibin magani har ya koma gida, yayin da ya rage daya matar wacce take samun kulawa a wani kebantaccen wuri dake babban asibitin koyarwa, da wasu daga cikin 'yan uwanta da aka ware, don mu'amalar su da ita.
Ya kara da cewa, ko a safiyar yau ma sai dai aka ba shi rahoton wasu karin mutane ukun da ake zargin sun harbu da cutar, wadanda yanzu haka ake gudanar da bincike a kansu.
Ya yi kira ga jama'a su taimakawa kokarin da gwamnati take yi wajen tsaftace muhallanci da kare kawunan su da iyalansu daga beraye.
Masana kiwon lafiya dai sun tabbatar da cewa, ana kamuwa da cutar zazzabin Lassa ne ta hanyar wasu nau'in beraye masu dogayen jela dake tsoma baki cikin ruwa ko abinci.
Zuma Times Hausa