Sanarwa ta musamman daga Darantan mulki na Gidan Rediyon jihar Kano, Malam Aliyu Tijjani Sakamakon rade radi da wasu suke yadawa game da dakatar da Malam Habibu Gwangwazo.
"Malam Habibu Gwangwazo ya karya dokokin gidan Rediyon ne na fitar da bayanai na sirri da yake a dakin adana bayanai na gidan rediyon.
"Wannan laifi da ya aikata ne ya sa hukumar gidan rediyon ta jihar Kano ta dakatar da shi na tsawon makonni biyu,
ba kuma ta kore shi ba ne, sannan kuma ba ta dakatar da albashinsa ba.
"Don haka muna kira da al'ummar jihar Kano da su yi watsi da wannan magana na cewa an sallame shi daga aiki saboda ya yabi Kwankwaso.
"Malam Habibu Gwangwazo har yanzu ma'aikacin gidan rediyon na jihar Kano ne", kamar yadda daraktan mulki na gidan rediyon na Kano, Malam Aliyu Tijjani ya bayyana.
Source Rariya