Kakakin rundunar sojojin Nijeriya Kanar Rabe Abubakar ya musanta zargin cewa rundunar ta tsare dan jaridar nan da ake nema ruwa a jallo Ahmed Salkida, inda ya ce ba su da masaniyar inda aka kai Salkida ko kuma su waye suka yi awun gaba da shi, yayin shigowar sa Nijeriya.
Idan ba ku manta ba dai mun kawo muku wani labari da ke bayyana cewa wasu jami'an tsaro sun kama dan jarida Ahmed Salkida, jim kadan bayan saukar sa a filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe.
Jami'an tsaron Nijeriya na bukatar binciken wannan dan jarida ne sakamakon dangantakar da yake da ita da mayakan Boko Haram, domin sanin hanyoyin da za a bi a ceto rayukan 'yan matan Chibok da mayakan suke garkuwa da su.
Source Zuma Times Hausa
Title :
Ba Mu Kama Ahmad Salkida Ba - Rundunar Sojan Nijeriya
Description : Kakakin rundunar sojojin Nijeriya Kanar Rabe Abubakar ya musanta zargin cewa rundunar ta tsare dan jaridar nan da ake nema ruwa a jallo Ahm...
Rating :
5