A Yanzu haka dai shugabar Radio Kano Hajiya Sa’adatu Babaji ta dakatar da shugaban ma’ajiyu na gidan radiyan Alhaji Habibu Musa Gwangwazo wai sabida an sanya wata waka inda aka yabbi kwankwaso a gidan radiyan.
A cewar wani maaikacin da yayi magana da mujallar daily trust wai laifin Alhaji Gwangwazo shine ya zabi wata waka wadda a cikinta a yabi tsohon gwamna Raniu Kwankwaso.
Ma aikaciyar dakke duty a ranar da aka sanya wakar Hajiya Furera Umar itama ta tsira da wasikar query.
Wannan dai shine sabuwa a jerin takalmin karfen da gwamnatin ganduje ke yi a Kano. A kwanakin bayane yan sanda suka rufe gidan lugard domin yunkurin hana auren zaurawa a jahar.
Title :
An Dakatar Da Ma'aikaci Gidan Rediyon Dan Yasa Wakar Yabo Kwankwaso
Description : A Yanzu haka dai shugabar Radio Kano Hajiya Sa’adatu Babaji ta dakatar da shugaban ma’ajiyu na gidan radiyan Alhaji Habibu Musa Gwangwazo wa...
Rating :
5