Daga Jaridar Rariya
Babban kamfanin gina layin dogo na kasar China ya bayyana cewa ya samu izinin soma aikin gina titin dogo a jihar Kano wanda zai lashe kimanin Dalar Amurka Bilyan $1.851.
A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a yau Litinin yace ya samu izini daga Gwamnatin tarayyar Nigera domin soma aikin titin jirgin kasan wanda zai kai tsawon kilomita 74.3 kuma ana sa ran jirgi zai rika gudu akan kilomita 100 duk sa'a daya kwatankwacin tafiya daga Lagos zuwa Ibadan a mintoci 72.
Kashi na farko dai na aikin zai dauki tsawon shekara Biyu a yayinda kashi na biyu na Shirin shima za'a kammala shi a tsawon shekaru Biyu.
Title :
Kamfanin Kasar China Zai Gina Titin Jirgin Kasa Mai Nisan Kilomita 74.3 A Kano
Description : Daga Jaridar Rariya Babban kamfanin gina layin dogo na kasar China ya bayyana cewa ya samu izinin soma aikin gina titin dogo a jihar Kano w...
Rating :
5