Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ya yi alkawarin sanya baki wajen ganin an kawo karshen rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam'iyyar adawa ta PDP.Tsohon Shugaban ya yi wannan ikirarin ne a lokacin ziyarar kwamitin amintattu na jam'iyyar a karkashin jagorancin Sanata Walid Jibrin inda ya nuna cewa ya rigaya ya fara tuntubar wasu da ke cikin rikicin.Ya kara da cewa al'ummar Nijeriya na son ganin jam'iyyar adawa mai karfi wadda za ta rika kalubalantar manufofin gwamnati ya kuma nuna takaicinsa kan yadda bangarorin suka rika zuwa kotuna don ganin sun yi rinjaye a rikicin.
Rariya