Jarumar 'yan wasan Nigerian Film Lola Alao ta canza addinin ta na kiristanci zuwa musulunci. Jarumar dai ta canza addinin nata ne a ranar Talata 19 ga watan yuli a Acadamic Of Propagation Nigeria wanda akafi sani da [ACADIP].
Jarumar har ila yau ta canza sunan ta zuwa Rhodiyat. Shugaban kungiyar Adepoju Yusuf shiya bayar da sanarwar labarin, ya kara da cewa, "godiya ya tabbata ga Allah; ku tayani yima Lola Alao (jarumar 'yar wasan Nigerian Film) murna, saboda a yau ta amshi kalmar shahada daga wajena. Kuma ta zabi Rhodiyat a matsayin sabon sunan ta. Allah ya yarda da ita amatsayin musulma, kuma yasa mata albarka akan duk wani abunda zatayi a rayuwanta, amin".
Alao dai ba itace ta farko a cikin yan wasan Nigerian Film data fara musulunta ba, akwai jaruma mai suna Lizzy Anjorin wanda ake ce mata Elizabeth Anjorin ada, ita ta fara musulinta harma taje aikin Hajji.