A jiya ne 15 /06 /2016 aka fara raba tallafin Na azumi Wanda Mai Girma Gwabnan jahar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar ESQ ya bada umarni tun satin da ya wuce,
wa masallatai a cikin Garin Bauchi da kewaye Kar kashin jagoranci komishina Na addinai ABDULLAHI MUHAMMAD IDRIS
A lokacin bayani Na bude taro, Sannan Kuma ya Kara dacewa Mai Girma Gwabnan jahar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar ESQ ya bada tallafi na ciyarwa wa masallatai ya acikin Garin Bauchi da kewaye. Domin Tallafa ma Al'umman jihar cikin Ramadan Domin samun Addu'ar Samun sauki cikin lamarin Gwamnatin jihar da kuma kasa Baki Daya
Komishinan ya Kara da cewa Mai Girma Gwabnan ya bada tallafi Sama da Naira miliyan ashirin Wanda za'a Raba wa masallatai ya.
Sannan Shugaban malamai Wanda zai jagoranci sauran malaman shine,
SHEKH ZUBAIRU ABUBAKAR MADAKI yayi karin bayani Kamar haka yace Gwamnati data dauki nauyin ciyar da masallatai Dari biyu da hamsin {250 }
sa banin shekaran da tawuce Wanda a 2015 Ramadan masallatai Dari da casa'in da biyar 195 aka ciyar, amma a wannan shekaran bisa kokari Na Mai Girma Gwabnan za'a ciyar da masallatai Dari biyu da hamsin {250 }
ya yabawa Mai Girma Gwabnan jahar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar ESQ Na Kara wa Adadin masallatai a cikin Garin Bauchi.
Malam Zubairu Madaki yayi karin bayani da cewa ko wani KaraMar hukuma am bata dama kudi da ta ciyar da masallatan da yake kananan hukumomin ta.
Malam Zubairu Madaki Kuma ya gaya wa Malamai cewa zasu bi masallatan da'aka basu wannan ciyar don suga yanda suka gudanar da kudin da aka basu.
Malam Zubairu Madaki yayi addu'an da cewa Kamar yadda muka fara azumi lafiya Allah yasa a gama lafiya.