Majalisar ministoci ta amince da sabon tsarin karbo basussuka daga cibiyoyin bada lamuni na kasashen waje a wani mataki na farfado da tattalin arziki da kuma samar da ababen more rayuwa.
Da take karin haske game da sabon tsarin, Ministar Kudi, Kemi Adeosun ta nuna cewa gwamnati ta dauki matakin ne saboda wa'adin tsohon tsarin da ake amfani da shi ya ciki.
Ta kara da cewa sabon tsarin zai fara aiki ne daga shekarar 2016 har zuwa 2019. Majalisar dai ta cimma wannan matsaya ne a zamanta na jiya a karkashin jagorancin Mukaddashin Shugaban Kasa, Osinbajo.
Title :
Majalisar Ministoci Ta Amince Da Sabon Tsarin Karbo Bashi Daga Waje
Description : Majalisar ministoci ta amince da sabon tsarin karbo basussuka daga cibiyoyin bada lamuni na kasashen waje a wani mataki na farfado da tatta...
Rating :
5