Daga Affan Bubu Abuya Na Jaridar Rariya
Gwamnonin kasar nan suna danne hakkokin Ma'aikata ga yaudara da suke yi, idan wannan rana ta zagayo za ka ji suna cewa za su biya Ma'aikata hakkokinsu har ma su biya 'yan fensho da giratuti, amma daga nan shike nan ba za su kara tunawa da Ma'aikata ba sai rana mai kamar ta jiya. Wato ranar da Gwamnatoci suke yaudarar Ma'aikata a wajen bikin ranar Ma'aikata, kuma gwamnatoci na amfani da shugaban nin kungiyar kwadago wajen kawar da tunanin Ma'aikata, sai ka ji kungiyar sun fito suna cewa dole gwamnati ta biya albashi mafi tsoka bayan albashi marar tsokar ma gwamnatocin ba sa biya. Duna haka ne dan batar da tunanin ma'aikaci kar ya tuna hakkin da yake bin gwamnati.
Uhm Ma'aikata gara ku suna yaudarar ku ma, domin akwai wadanda ba su da aiki ana yi musu alkawari lokacin yakin neman zabe, daga sun dare kujera ba sa tunawa da alkawarin da suka yi.
Abun takaici idan za'a bada aiki sai a boye, idan an bayyana duniya za ta gane yawan marasa aiki a Nijeriya. Misali Gwamnatin Tarayya ta bada damar daukar yan sanda 10,000 amma abun ban takaici cikin sati uku da aka bude yanar gizo na daukar 'yan sanda, bincike ya nuna cewa sama da mutun 700,000 ne suke neman shiga aikin na 'yan sanda, duk cewa mutun 10,000 kawai ake bukata.
Allah ya kyauta, amma inganta wuta da masana'antu shine abun da ya dace gwamnati ta sa gaba, Allah ya ba su iko. Amin.
Title :
Ranar Ma'aikata Ko Ranar Yaudarar Ma'aikata?
Description : Daga Affan Bubu Abuya Na Jaridar Rariya Gwamnonin kasar nan suna danne hakkokin Ma'aikata ga yaudara da suke yi, idan wannan rana ta z...
Rating :
5