An bayyana gazawar gwamnatin Muhammadu Buhari, musamman a fannin rashin tabuka wani abin a zo a gani a shekara daya da ta yi a bisa karagar mulki da cewa ya bayyana karara zaben shekara ta 2019, ‘yan Nijeriya za su dawo daga rakiyar jam’iyyar APC a kowane mataki.
Kalaman hakan sun fito ne daga bakin Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido a yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron zaben Shugabannin jam’iyyar PDP na yankin jihohin Arewa Maso Yamma, wanda suka hada da, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Jigawa, Sokoto, da kuma Jihar Zamfara, wanda ya gudana a dakin taro da ke kasuwar Duniya ta Kaduna.
Alhaji Sule Lamido ya kara da bayyana cewa, “yanzu dai dukkan ‘yan Nijeriya sun yarda kuma sun gamsu da cewa Buhari da jam’iyyarsa ta APC, mulkin Nijeriya ya fi karfin su, ba za su iya ba, sun yaudari talakawan Nijeriya, sun iza su sun gaza fidda su. Dama na riga na san da haka, shi ya sa na yi rantsuwar da ba zan yi mata kaffara ba cewa, jam’iyya mai adalci ta talakawa, ita ce Jam’iyyar PDP, kuma za ta dawo kan madafun iko a shekarar 2019 In sha Allah.”
Title :
Na Yi Rantsuwar Da Babu Kaffara, PDP Ce Za Ta Lashe Zabukan 2019 —Sule Lamido
Description : An bayyana gazawar gwamnatin Muhammadu Buhari, musamman a fannin rashin tabuka wani abin a zo a gani a shekara daya da ta yi a bisa karagar...
Rating :
5