As-salamu alaikum malam Allah ya karama maka himma na isar da Sakon MAI ALBARKA ANNABI (SALLALLAHU ALAIHI WA ALIHI WA SALLAM)
Malam wai malamman nan masu yawo kasuwannai da sauran masallatai ranar jumu'a, suyi karatu suce ko akwai mai tambaya in akwai mai tambaya sai mai tambaya ya bada N100 sai a warware masa tambayar sa da abinda ta kunsa
Misali in sata aka yiwa mutum sai ya fadi abinda aka sake kuma yayi bayani akai ko kuma in namiji ko mace in sun gagara aure sai yayi bayani akai ko kuma in matsala ce tsakanin ma-aurata sai yayi bayani akai kuma yafadi dalilin da ya kawo matsalan da saurar wasu matsalolin
Abin tambaya anan wadanan malammai ne ko bokaye ne?
Miye hukunci mutanan dake zuwa wurin wadanan mutanan
Allah ya bada ikon amsa daga wani bawan Allah
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Kamar yadda Manzon Allah (saww) yayi bayani acikin San hin hadithi, yace : "DUK WANDA YAJE WAJEN BOKA KO 'DAN DUBA, KUMA YA GASKATASHI CIKIN ABINDA YAKE FA'DA, TO HAKIKA YA KAFIRCE MA ABINDA ANNABI MUHAMMAD (SAWW) YAZO DASHI"
(Muslim ne ya ruwaito).
Su wadannan mutanen da kake fada, lallai 'Yan duba ne. Kuma duk wanda yaje wajensu kuma ya gaskata abinda suka gaya masa to hakika ya kafirce ma abinda Manzon Allah (saww) yazo dashi.
Bokaye da 'Yan duba dukkaninsu suna Qaryar sanin gaibu ne. Don haka suka zama Makiyan Allah. Kuma su wakilai ne ga shaitan da shaitanci. Don haka guje musu ya zama Wajibi.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU (14-04-2016).
Title :
Hukuncin Zuwa Wajen Yan Duba
Description : As-salamu alaikum malam Allah ya karama maka himma na isar da Sakon MAI ALBARKA ANNABI (SALLALLAHU ALAIHI WA ALIHI WA SALLAM) Malam wai mal...
Rating :
5