A yau shugaban majalisar Dattawa, Sanat Bukola Saraki, ya gurfana a gaban kotun CCT inda babu wani Sanatan daya roko shi zuwa majalisar kamar yadda suka saba.
Idan za’a iya tunawa, a ranar farko da aka fara Shari’ar, Sanatoci 50 suka roko Sanata Bukola Saraki kotun domin su nuna goyon bayan su.
A rana ta 2, Sanatoci 80 ne suka rako Saraki kotun ta CCT wadda take a Jabi, a nan garin Abuja, domin nuna goyon bayan su ga shugaban majalisar.
Ku karanta Daga Hamsin Zuwa Biyu: Sanatoci Biyu Ne Suka Rako Saraki Zuwa Kotun
A ranar ta 3, ranar Juma’a 11 ga watan Maris, Santoci 30 ne suka roko ahugaban majalisar zuwa cigaba da shari’ar tashi.
Daga baya ne suka cigaba da ragewa inda a makin daya wuce Sanatoci ne kawai suka rako shi.
A yau kuma babu wani Sanatan daya biyo Saraki zuwa Shari’ar tashi.
Haka zalika a nakon daya wuce ne wasu sanatoci suka nemi a fasa cigaba da kokarun canza dokar CCB wadda ta bada dama ana bincikar Sanata Bukola Saraki. Daga cikin Snatocin da suka hana canza dokar sun hada da Sanata Ben Bruce, Sanata Shehu Sani da sauran su.
Idan za’a tunawa, Sanata Bukola Saraki ya zama shugaban majalisar inda ake zargin cewa ya hada kai da wasu Sanatoci na PDP inda ya samu kujerar. Wannan ya jawo mashi kalubale daga wasu manyan jam’iyarra.
A wani labarin kuma, shugaban kass Myahammadu Buhari gana da shugabanin majalisar Najeriya inda suka warware matsalolin dake tare da kasafin kudi na 2016.
Title :
Babu Sanatan Da ya Rako Saraki Zuwa Kotun CCT A Yau
Description : A yau shugaban majalisar Dattawa, Sanat Bukola Saraki, ya gurfana a gaban kotun CCT inda babu wani Sanatan daya roko shi zuwa majalisar kama...
Rating :
5