Tare dani..Abu Abdullah
Gawar Hajiya a cikin makara a farfajiyar gida, yayin da jama’a ke tsaye jefi-jefi wasu na matsar hawaye wasu kuma a cikin yanayi irin na alhini, Dan Hajiya da ankwa a hannu ya shigo gidan, Mudi da Tanko suna biye da shi , har ya je jikin makarar ya durkusa yana kuka.
”Hajiya kullum maganar ki bata wuce ta yadda zan inganta rayuwata, a kan haka kika zauna da damuwa tsawon lokaci. Abun da ke faruwa dani a yanzu na sa a raina cewa yana da nasaba da alhakinki da kin bin umarnin ki, Allah ya gafarta miki, na miki alkawarin bayan wannan al’amarin ba zan sake waiwayar irin rayuwata ta baya ba, zan gina wata sabuwa.”
Mudi da Tanko suka hada hada ido, Tanko ya ce
”Ashe mutumen da yake a gabar fukantar hukuncin mutuwa ma yana da sauran fata?”
Ya dago kai ya kalle su yana zubar da hawaye, Mudi ya kamo hannunsa ya tashe shi tsaye
”Ba ka da sauran lokaci na ganawa da matacciyar mahaifiyarka, taso mu tafi ka fuskanci kalubalen da ke gabanka.”
.
POLICE STATION/ ENFORCEMENT ROOM
Mudi yana dukan Dan Hajiya da kulki, yayin da shi kuma yake ta babatun cewa
“Ba ni na kashe shi ba.”
”Ba za ka fadi gaskiya ba.”
”Iya gaskiyata nake fada maka, ba ni na kashe shi ba.”
“Duk wani mai laifi haka yake fada, sai ya ji wahala sa’an nan yake fadar gaskiya, ba za ka fada ba?”
Mudi ya ci gaba da sukansa, shi ma ya ci gaba da ihunsa.
“Ba ni kashe shi ba.”
”In ba kai ba ne, a ina ka boye matar tasa abokiyar aikin naka.”
Ya tsaya da dukansa.
”Wallahi lokacin da kuka ganni da ita, wannan ne lokaci na farko da na fara ganinta.”
”Na gaji da jin wannan tatsuniyar ta ka, ka yiwa kan ka gatan fadar gaskiya, kila hakan ya sa hukuncinka ya zamo sassauka.”
”Ranka ya dade, bar sa min magana a bakina, ban yi kisa ba ko kashe ni za’a yi ba zan amsa wannan hukuncin ba.”
Mudi ya ci gaba da dukansa
.
POLICE STATION/ DPO OFFICE
Tanko ya shigo cikin ofis din ya mikawa DPO wata takarda, YA fara nazartar ta na dan wani lokaci kafin Tankon ya ce da shi
“Sakamakon gwajin zayyanar yatsun da ke jikin wukar ne(thumb-print), amma kuma abun mamakin shine yazo dai-dai da na suspect din mu na yanzu.
DPOn ya dago kai ya kalle shi
“In haka ne mene ne alakarsa da gujajjiyar matar marigayin, wanne dalili ne ya sa shi kashe shi?”
”Abun da muke son ganiwa kenan yanzu.”
“Kwarai, haka ne ya dace.”
Tanko ya masa salute sa’an nan ya juya ya fita.
Hujjojin da suka samu a hannu ko da kuwa kirkirarru ne sun nuna cewa Dan Hajiya ne ya yi kisa, ba wanda ya zama shaidar cewa dan Hajiya ba zai iya yin haka ba, in ma akwai abun da yafi haka zai iya yi.
Ina Sadiya? Makashiyar da ta gudu ta bar shi, ya taka sawunta ya ke fuskantar barazanar amsar hukuncin kisa!
BAYAN WATA DAYA
Linda a zaune a kan bencin bayan kanta, bayan wani lokaci Dan Hajiya a gaba Tanko yana biye da shi har zuwa in da Linda take, Dan Hajiya ya zauna a kusa da ita ya bi ta da murmushinn karfi da laushin hali, sa’an nan ya kawar da kansa
“Kin ga dai wata daya da faruwar wannan al’amarin har yanzu ba wani ci gaba, nine a cikin zargi.”
“Damuwata kenan.”
Suka yi shiru na wani lokaci, Dan Hajiya ya ja numfashi sa’an nan ya kalli Linda ya sunkui da kansa.
”Linda kin san mai nake so da ke?”
”A’a sai ka fada.”
”Rasuwar Mahaifiyata da kuma halin da nake ciki a yanzu ya koya mini darrusa da dama a rayuwata, har ina tunanin da ma a ce a na dawo da gaba baya da na chanza mummunar rayuwata ta baya da wata sabuwa.”
Ta kalle shi da sanyin jiki
“Haka ne dama, nima duk jikina yayi sanyi.”
Ya ci gaba
“Linda na fahimci cewa rayuwar duniyar nan ba dawwamammiya ba ce, kuma in Allah ya ga dama sai ya bar ka ka yi ta tsula iya shegenka, in kuma ya so ka da shiriya sai ya saka a takunkumin da za ka fahimci kuskurenka, ni dai yanzu abun da nake so na sanar da ke shine na fahimci cewa rayuwar da muka yi ta baya matacciya ce, yanzu na fahimci gaskiya, Linda ki tuba ki koma gida ki nemi gafarar magabatanki.”
Linda ta zaro ido
”Nima ina wannan tunanin, amma idan na tuna ba lallai Mahaifina ya yafe mini ba saboda kuncin da na jefa shi a ciki, sai na ji jikina yayi sanyi.”
”Ki tuba da kyakkyawar niyya, ki yi nadamar ayyukan ki na baya, ki je wa Mahaifinki cikin kas-kantar da kai kina mai nadamar abun da kika aikata masa, in Allah ya yarda zai amshe ki.”
”Shikenan na gode da shawararka, in Allah ya yarda zan yi hakan.”
A dai-dai nan Tanko ya zo wajen yana duba lokaci a agogo.
”Lokaci yayi Hajiya, sai kuma wani lokacin.”
Linda ta kalli Dan Hajiya tana zubar da hawaye.
”Shikenan zan tafi, zan koma gida, sai wani lokacin kuma in da rabon ganawa.”
Ya bi ta da kallo
”Shikenan, Allah ya kaddara haduwar mu a lokaci na gaba, idan Allah ya yi fita ta zan nemi garinku, za ki ganni.”
Tanko ya tashe shi ya hankada keyarsa, ta tsyaa ta bi shi da kallo. Bayan sun dan yi nisa, Dan Hajiya ya tsaya ya wiago suka hada ido da Linda
“Linda mene ne sunanki na gaskiya.”
Ta daga kanta sama tana tunani
“Safara’u, kai ina ga ba haka ba ne, wai sunana Kulu.”
.
BAYAN SATI BIYU
Mudi a teburin Mai Shayi, Sadiya ta zo ta wuce ta gabansa da kirkirarriyar siffar tsoffinta, ya bi ta da kallo, furfurar da ta lika ta auduga a girarta ta fado kasa, Mudi ya sau baki ya bi ta da kallo, ya daga kai tare da tunanin a in da ya san ta. Ya sauko da kan tare da dauko photon da ke aljihunsa, ya duba, ya ga yayi kama da Sadiyar zahiri. Ya dago kansa, yana dagowa zai tarad da ba ta nan sai filin gurbin.
Ya tashi da sauri ya bi bayanta.
.
KWARARO
Sadiya tana tafiya a cikin kwararon har ta zo dai-dai wani Kango, ta shiga ciki ta samu guri ta rakube, a waje kuma Mudi yana ta waige-waige,harya shigo cikin kangon, ya na ci gaba da waige-waigensa , har ya shigo in da Sadiya take a rakube, ya waiga kamar zai gano ta sai kuma ya kara juyawa ya fita, bayan wani lokaci da fitarsa, Sadiya za ta mike ta fito ta ci gaba da tafiyarta.
A wannan lokacin , ga Dan Hajiya can a kotu a na shirin yanke masa hukuncin kisa saboda ba wata hujja da ta nuna cewa ba shi ya kashe Mubarak ba, kansa ya dau zafi, ya na so yayi kuka ko ya samu sa’ida amma ya kasa.
Ya kalli alkali ya ce
“Ranka ya dade, ina neman alfarma.”
“Ta me?”
“Kafin mutuwata, a samo mini kwalin sigari Aspen daya, a bani minti talatin.”
Ya nemi tuba da nadamarsa, sun bace bat! Yana ganin Aspen ita ce kawai za ta rage masa tururin zuciyarsa
hahaha wato dan iska dan iskane koda ALAHIRANE...
Seda safen ku...
Kasance da mu akodayaushe dan JOining din mu ko kuma