.
Ba ka buqatar a gaya maka cewa YM Bello yana hutawa, kai da ganin shigarsa ka san an ci uban Naira, don wata shadda ta kece raini ya watso, qirar Holand, ta sha aikin hannu, ga aljuhan gefen rigar sun dan dago da Nairori, ko da yake bai cika son aski sosai ba amma Jummai tana son abinta haka, yau dai ya aske qasumbarsa gaba daya sai ya bar wani zirin saje wanda ya sada suman kansa da gemu, tun kafin ya bude qofar motar har wani qamshi ya gama zagayen wurin, ko da wani irin turare yake aiki Allahu A'alam, agogon hannunsa kuwa tabbas na zinare ne, shi kadai zai iya gaya maka qasar da aka sayo da kudin da aka saya, don shi ke sanye da shi, ya dan dada gyara tsayuwar motar, ya turo qafarsa daya waje kamar ba zai sauka ba, hakan za ta sa kowa ya iya kallon adonsa, safarsa ma kawai abar kallo ce to bare kuma takalmin, irin wannan takalman ko a Italy sai an jajurce wajen nemansu, don wani irin sabon salo ne da su, ga su dai takalmi ne masu rufi amma suna da sifar sandal.
.
A gefe guda kuma su Jummai suka miqe cikin sauri suka nufi inda ya tsaya yana hangensu, da isar su ya bude musu qofa suka fada ciki, wata sabuwar qirar Range Rover Evoque ce ta sha wani irin fenti mai kama da kunun kanwa, ga alama ta masammance don ko lambarta ta Abuja ce "Sorry kun jima kuna jira ta ko?" In jishi, yana magana cikin jiji da kai da qasaita, wani sa'in masu hannu da shuni sukan yi haka, ko masu iko, ko samari a gaban 'yanmata, masamman in sun sami hadin kan 'yammatan sosai-sosai "Na dan tsaya duba wani aiki ne da ake so ya bar qasannan sha Biyu"
.
Yana fadin haka ya yi sauri ya duba agogonsa, galibin wadan da lokaci yake musu qaranci za ka taras da su kullun cikin duba agogo suke "Na san yanzu haka ya kusa isa Paris, kin san Germany sun fi kowa tsari in dai batun kwangila ne" Jummai sai murmushi kawai take yi tana kallonsa da gefen ido, wace ko a Arewacin Nigeria ina ta sani? To bare kuma a ce Paris, sai dai duk da haka 'yar makaranta ce, ta san capital city na qasashe da dama "Ok Berlin dai ko? Paris ai capital din France ne" in ji Mari.
.
Nan fa YM ya gano cewa ya fa buga, to amma da yake namiji ne sai ya kada baki ya ce "Oh yes! Abin da nake nufi zai bi ta Paris ne kafin a qarshe a isar da shi can Ber... I mean can Germany din, ina ma da wata mota qirar Aston Martina da za a kawo min don shan iska" Mari ta kalli Jummai amma ko daga kai ta kasa yi bare su yi ido Biyu, abin da babu shakka a kai tana matuqar qaunar YM Bello, shi ma za a iya cewa yana qaunarta, ko da yake tun haduwarsu har zuwa yau bai taba yi mata wani qasaitaccen abu wanda zai nuna cewa shi hamshaqin mai kudi ne ba, amma gani ya kori ji, don motocin da yake hawa kawai sun isa ka gane irin dimbin dukiyar da yake da ita, shekaran jiya ma a cikin Jeep Grand Cherokee ya zo, wata sabuwar yayi mai saukakken gaba dinnan.
.
Ya dan juya ya kalle su "Ya kamata a ce na samo mana dan Mult ko? Me kuke sha ne? Evamult, Multina ko Multi Guiness? Ga su nan dai sai wanda kuka zaba, unguwannan taku ba a sayar da abubuwa masu kyau, irin su matsattsen inabi da sauransu, koda yake mu ma can wurimmu haka abin yake don haka na yanke shawarar yin connecting da kamfanin sai su riqa kai min gida" da yake bai kama hanyar zuwa shagon ba, sai Mari ta amshe "Ba sai ka sayo mana ba, ba zan so ka tafi ka bar masoyiyar taka tana zaman jiranka ba, ba ni kawai na yo muku order, ko me kika ce J baby?" Jummai ta dan yi murmushi "A'a bar shi ya je da kansa na san ya kwana Biyu bai yi exercise ba"
.
Kafin Mari ta sake cewa wani abu har YM Bello ya yi waje ya nufi wani babban super market yana tafiya kamar ba zai taka qasa ba "Su Jummai an yi hankali, wallahi ki ji tsoron Allah, ban da coge, kin ga yadda kika zama kamar wata mumina wannan ko Amatu sai haka" in ji Mari, Jummai ta kai mata duka "Ban son iskanci da ma ya halina yake? Ni da ma a gaban saurayina ban ciki sakin jiki sosai ba, kin san yana da kyau mutum ya dan daga ajinsa don kada a raina shi" Mari ta harare ta "Bude Idanu, da Mari kike magana, kina nufin haka kike yi a gaban JY? Wanda har ruwan wanka da na wanki yake debo miki ne za ki ce wani kina girmama shi, ni wallahi zargina kawai kuke yi da yake kun raina qurata amma wallahi kowace gauta ja ce, ba zan ba ki shawarar ki manta da YM ba, don ko ni ce na sami wannan wallahi tamau zan riqe kayana, don sakaci da irinsu asarar duniya da ta lahira ce"
.
Ita kuwa Jummai kallon qofar super market din kawai take yi ta ga fitowarsa "Wai ma ba haka ba, Jummai shin wannan MB din mutumin ina ne? Na san dai da a ce Bakano ne ya kamata a ce mun san mahaifinsa, don da ganinsa ba qaramin mutum ba ne, duk manyan masu kudin Kano sanannu ne, don in ba ka rufa ka ta da kai ba ne ba a maganarka"a
.
Kafin Jummai ta ba ta amsa har YM Bello ya iso jikin motar, don haka hankalinsu ya koma kansa "Gaskiya 'yan Nigeria ba su iya kasuwanci ba, ki je Dubai ki ga yadda ake haba-haba da customer, ke kya ce zai saye kayan duka ne, amma mu nan VIP ma ba wanda yake kula da shi, ko magana ka yi sai ka ga kamar za a ba ka kyauta, ni don kar na fito ne kawai hannu banza da na bar musu kayansu na yi gaba, irin wannan dole mutum ya yi zuciya ya hada nasa na masamman a gida, in ba haka ba ran da mutum ya yi wasu manyan baqi daga wata qasa kunyata shi kawai za su yi!" "Kai kuwa ka cika damuwa a kan dan qaramin abu, mu dai qasarmu ta fi mana kowace qasa gaskiya, kuma ko Dubai din da kake magana ai ba don Allah suke yi ba" in ji Jummai.
.
YM ya dan kurbi Multina ya sako qafa qasa "Amma ke ma da abin dariya wallahi, a ina kika taba ganin an yi abu don Allah? Ai language din da ake communicating da shi kenan Naira, ita ce kawai za ta yi maka maganin wulaqanci, ko wadannan yaran da suke zama a shagonnan idan ina son su san ko ni waye, ba wani abin bata lokaci ba ne watsa musu kawai zan yi, don dai ina son na riqa yin komai da kaina ne, ba na son girman kai!"