Duk da nasarar da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta yi, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sha jifa a wurin magoya bayanta, inda suka dinga jifarsa da ledar fiyawata, takalma da sauransu. Gwamnan ya zo filin wasa na Sani Abacha ne dake Kofar Mata domin kallon wasa tsakanin Pillars din da Wikki Tourist ta jihar Bauchi.
An tashi biyu da daya ne a wasan. Amma bayan alkalin wasa ya hura tashi, sai magoya bayan Kano Pillars din suka soma ihun "ba ma yi" ga gwamnan da sauran tawagarsa, wanda a dalilin haka jami'an tsaro suka zagaye motocinsa har ya bar filin wasan.
A yayin jin ta bakin shugaban magoya bayan kungiyar, Bashir Jide bai dauki waya ba, amma wata majiya dake kusanci da shi ta bayyana cewa fushin da magoya bayan kungigar suka nunawa gwamnan, sun yi ne bisa zargin da suke yi wa gwamnan da hukumar gudanarwar kungiyar kan rashin sayen ingantattun 'yan wasan da za su bunkasan kungiyar.
Haka kuma magoya bayan kungiyar sun nuna rashin jin dadinsu na kasancewar Kabiru Baita a matsayon shugaban kungiyar, wanda suke zarginsa da nuna bambanci ga wasu daga cikin manyam 'yan wasan kungiyar.