** Doguwar hanya ce me ma2kar fadi wacce ta kasance mikakkiya sambal! Ta yadda zaka iya hango abinda yake nesa, shimfidaddiyar kwaltar dake daukar ido da babu ramuka ko kwazazzabai akanta ya karawa hanyar fasali da kyan yanayi.
Idan ka kalli hagu da daman titin kuwa kyawawan kantuna ne kala-kala duk inda ka gifta, tsakiyar kwaltar kuwa motocine manya da kanana, tsala-tsala wadanda daka gansu kasan mallakar masu hannu da shuni ne da kuma na masu rangwamen hali harma da taxi-taxi na haya dake ta tallar wurin da suka dosa.
Hakadai suketa giftawa wata nabin wata.
Daga gefen titin kadan kuwa mutane dake tafiya a kasa ne keta kaiwa da kawowa kowa na nufar inda ya dosa, a cikin wadanda ke tafiyar kasan itama take sai sauri take tamkar zata tashi sararin samaniya.
Hannunta na rike da bakar leda babba irinta store wadda da alama kaya ne a cknta, hankalinta gaba daya yayi gida kasancewar yamma ta doso don akalla karfe 6:00pm na yamma ta kawo jiki.
Sai dai duk da saurin da takeyi baisa ta koda nuna alamun ta tsaya don tarar mota ba, illa saurin da take zubawa da kafarta duk da cewa masu taxi nata kawo mata talla ganin cewa bata dace koyin kama da tafiyar kasa ba.
KALLO DAYA zakayi mata kasan bata ckn walwala ko farin ciki hasalima ckn damuwa take tamkar zata fashe da kuka, sai dai duk halin da take ciki bai bayyana muni a gareta ba wata kila hakan na nuna tsantsar kyawun da Allah yayi mata ne.
Domin kuwa farilla ne ga duk wanda ya kalleta ya sake kallonta, ta kasance ba fara ba amma ba zaka kirata baka can ba wanda hakan ya dace da yanayinta.
Kusan komai madaidaicine a tare da ita, jikinta rufe yake da ingattacciyar sutura ta kamala data dace da addini da kuma yanayinta.
*A hankali ta saki doguwar hanyar da take bi izuwa wata y'ar siririya kwalta da tayi kwana hannunta na hagu, babu mutane sosai a hanyar hakan yasa ta kara saurin tafiyar domin yanzu ta tabbatar ba me ganinta.
Sai da tayi tafiya kamar ta mintina goma tana tabin kwane-kwanen hanyar da take bi, jin karar worn da tayi a bayanta yasata ratsewa ta koma gefe motar ta wuce ta gabanta.
Kasancewar lkcn damuna ne ruwa na kwanciya a yan ramukan dake samuwa a mafi yawan hanyoyi musamman na layuka irin wadannan hakan yasa Bisa AKASI tayar motar ta shiga ramin da ruwa ke kwance a cknsa wanda yayi fallatsi kai tsaye ga inda kamilalliyar budurwar ta ratse don baiwa motar damar wucewa, ilahirin jikinta kuwa ya baci da ruwan wanda ya kasance ba ruwa kamar saura ba hade yake da kasa.
Tayi saurin rintse ido ckn tsananin takaici ta bude idanun nata tabi jikinta da kallo yadda yayi ma2kar baci, WATA SABUWA kenan ita da take tfyr kafa ga kaya a hannunta, gashi ta gaji ga bata da abin hawa mota kuma gashi jikinta ya baci ta yadda zataji kunyar tfy a haka ma2ka wasu ma ai sai suyi mata kallon zararriya.
Damuwarta ta linka tada sosai irin wacce ita kanta ta tabbatar ta bata taba yin irinta ba, da sauri ta daga kanta tabi motar data gifta din da kallo wacce tuni ta tsaya cak!! Tare da dawowa da baya a hankali ta sake tsayawa kofar motar ta bude a hankali wani matashin saurayi kyakykyawa ya fito daga tsaleliyar motar.
Kallo daya zakayi masa daga shi har motar tasa kasan DAN KWALISA ne, yayi saurin kauda glass din dake idonsa da cewa "inna-lillahi wa inna ilaihir-raji'un", sanda yafi jikinta da kallo.
A dai-dai lkcn ckn fusata byn ta gama binsa da kll da muryarta data banbanta ma2ka data kowa domin daban-daban take fita, sanyayya da sai ka saurara sosai zaka fahimci me take fada, tace " haba mlm!! Amma ka cuceni wlh ka gama dani.
Kai mahaukacine??
Baka gani ko makahone kai??
Ji fa yadda ka bata ni??
Duk fadin hanyar nan sai ka biyo tanan inda nake sbd dama akwai mugunta a ranka naka batamin ko??
To kayi kaji dadi amma ka sani Akwai ALLAH!!
Dan iska!! Macuci!! Azzalumi!! kawai...
Allah ya qara dawo dani...
Dan samun rubu tun mu akoda yaushe shigo nan
Like us On Facebook https://www.facebook.com/1arewa
Follow Us Twitter https://www.twitter.com/1arewa_official
Follow Us Instagram https://www.instagram.com/1arewa
Subcribe Our Youtube Channel https://www.youtube.com/1arewamk