RIKICIN PDP: Shekarau, Sule Lamido, Makarfi, Yuguda, Mantu, Nnamani Da Sauransu Na Shirin Kafa Sabuwar Jam'iyya
Sakamakon rikicin shugabanci da yake ci gaba da kunno kai a jam'iyyar adawa ta PDP, alamu sun bayyana cewa wasu daga cikin shugabanninta sun yi zama domin kafa wata sabuwar jam'iyyar.
Binciken da majiyarmu ta Sunda Trust ta yi, ta gano cewa tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan ilmi, Malam Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido da kuma tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijai, Ibrahim Mantu suna daga cikin wadanda za su kafa sabuwar jam'iyyar.
Sauran sun hada da tsohon ministan Abuja, Sanata Bala Mohammed (Kauran Bauchi), tsohon mataimakin gwamna a jihar Sokoto, Ahmed Muhammad Gusau, tsohon gwamnan jihar Bauchi, Isa Yuguda, tsohon gwamnan jihar Rivers, Donald Duke da kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Makarfi.
Sauran sun hada da Sanata Ibrahim Ida, Adamu Maina Waziri, Ibrahim Idris, Aminu Wali, Abba Dabo, John Odey da Aniete Okon. Majiyar ta mu ta kara da bayyana cewa tsohon shugaban majalisar dattijai, Ken Nnamani, shine jagoran tawagar.
Bincike ya nuna cewa Malam Shekarau ya jagoranci wasu mutane 23 daga cikin masu shirin kafa sabuwar jam'iyyar a wani zama da suka yi a gidansa dake Abuja a makon da ya gabata, sannan kuma a wasu lokutan sukan gudanar da zama a ofishin Nnamani.
Kusan tun daga lokacin da jam'iyyar adawa ta PDP ta fadi a zaben shugaban kasa na 2015 ne, rikici ya ci gsba da kunno kai a tsakanin shugabannin jam'iyyar. A ranar 25 ga watan Mayu, 2015, shugaban jam'iyyar Adamu Mu'azu ya yi murabus, bayan wasu membobin jam'iyyar sun zarge shi da taka rawa wajen faduwar jam'iyyar a zabe.
Title :
Wasu Yan PDP Na Shirin Kafa Sabuwar Jam'iyya
Description : RIKICIN PDP: Shekarau, Sule Lamido, Makarfi, Yuguda, Mantu, Nnamani Da Sauransu Na Shirin Kafa Sabuwar Jam'iyya Sakamakon rikicin shuga...
Rating :
5