Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa duk tafiye-tafiyen da yake zuwa kasashen waje babu na banza.
Buhari ya bayyana hakan ne sakamakon korafe-korafen da wasu ke yi game da tafiye-tafiyen da yake yi zuwa kasashen waje.
Ya ce yawancin tafiye-tafiyen sun kunshi siyasa ne da kuma harkar tattalin arziki.
Buhari ya bayyana hakan ne a birnin Landon a ranar Juma'a a yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai na Nijeriya jim kadan kafin ya bayyana zuwa hutunsa.
Idan ba a mance ba, a makon da ya gabata gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya ja hankalin shugaba Buhari da ya zauna a gida ya mulki al'ummarsa maimakon tafiye-tafiyen da yake, wadanda ya bayyana wasu daga cikin su a matsayin marasa amfani.