Wasu daga cikin shugabannin al'ummar Arewa mazauna Legas sun ce za su hada hannun da lauyoyi da kuma kungiyoyin kare hakkin bil'adama domin kwato hakkokin jama'arsu a Legas, kamar yadda majiyarmu ta BBC ta tawaito.
Shugabannin sun yi zargin cewa ana kama wasu daga cikin kananan 'yan kasuwa da kuma mazauna yankuna a birnin ba tare da tantance masu laifi ne ko kuma akasin haka ba.
Wannan mataki dai na zuwa ne bayan wani samame da jami'an tsaro na 'yan sanda a jihar su ka kai in da suka yi awon-gaba da mutane kimanin dari biyu.
Shugabannin sun ce da sannu a hankali yanzu an kwace ko kange yankunan da al'ummar arewaci da kuma 'yanci rani ke rike da su.
Sai dai bincike ya nuna cewa ba wai wuraren da al'ummar arewa kawai gwamnatin jihar Legos ke kwace ba, lamarin na shafar Yarabawa ma.
Hukuma ta musamman da gwamnatin jihar ta kafa mai dauke da jami'an 'yan sanda da aka dorawa nauyin tsaftace jihar, ta ce duk wuraren da ta ke kai farmakin ta na da kwararan shaidun da ke nuna cewa akwai bata gari a wajen
Title :
An Soma Kama 'Yan Arewa Mazauna Jihar Lagos
Description : Wasu daga cikin shugabannin al'ummar Arewa mazauna Legas sun ce za su hada hannun da lauyoyi da kuma kungiyoyin kare hakkin bil'adam...
Rating :
5