DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar, ya yaba gami da jinjinawa kokari da kwazo na Kungiyar majalisar koli ta harkokin addini Kirista a Nijeriya, sakamakon himmatuwa da ta yi na ganin zaman lafiya da lumana ya ci gaba da wanzuwa a tsakanin mabiya manyan Addinan nan biyu, Musulunci da Kiristanci.
Sarkin Musulmin ya yi wannan yabon ne, a lokacin da yake karbar bakuncin wakilan kungiyar majalisar koli ta Kiristocin, a wata ziyara da suka kawo masa a gidansa dake Unguwar Sarki a garin Kaduna.
Sa'ad Abubakar ya ci gaba da cewar, babu shakka cigaban kasa da bunkasarta basu samuwa matukar babu zaman lafiya a tsakanin jama'ar kasa, a domin haka ya kara yabawa namijin kokari da shugabannin Kiristocin sukeyi ta hanyar wayar da kawunan mabiyansu muhimmacin zaman tare da sauran jama'a.
Tun farko da yake gabatar da jawabi, shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Kirista a Nijeriya, Shugaba Emmanuel Udopia, ya ce sun kawo ziyara wajen Sarkin Musulmi ne domin nuna jin dadi da yaba masa dangane da yadda yake gudanar da jagorancin jama'arsa a cikin tsari da adalci, sannan kuma su nemi sanya albarka a wajen sa a matsayin sa na Dottijo wanda ba ya kyamar Kiristoci.
Title :
Sarkin Musulmi Ya Jinjinawa Kokarin Dattawan Kiristocin Nijeriya
Description : DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar, ya yaba gami da jinjinawa kokari da kwazo na Kungiyar ma...
Rating :
5