Bayan awanni takwas da hukumar EFCC ta saki na hannun daman shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma tsohon dan takarar gwamnan Kano a karkashin jam'iyyar APC, wato Kanal Jafaru Lawal Isa bayan ta cika hannu da shi, hakan ya sa jam'iyyar adawa ta PDP ta tabbatar da zargin da take yi wa shugaban kasa na farautar membobin PDP kadai kan badakalar sayen makaman.
Jam'iyyar ta kawo hujja da cewa har zuwa yanzu babban sakataren ta Olisa Metuh yana tsare a hannu hukumar EFCC ba tare da an gurfanar da shi a gaban kotu ba, bisa zargin da ake yi masa da karbar wani kaso daga cikin kudin sayen makamai.
Title :
Sake Ja'afaru Isa Ya Nuna Cewa 'Yan PDP Kadai Buhari Yake Farauta - Jam'iyyar PDP
Description : Bayan awanni takwas da hukumar EFCC ta saki na hannun daman shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma tsohon dan takarar gwamnan Kano a karkashin...
Rating :
5