Komitin da aka kafa don binciken yadda tsohon mai bada shawara kan harkokin tsaro ga tsohon shugaban kasa
Komitin da aka kafa don binciken yadda tsohon mai bada shawara kan harkokin tsaro ga tsohon shugaban kasa ya rabbaba kudadeb da aka ware don sayan makamai ya bukaci kamfanoni 241 da suke da dangantaka da kudaden da su zo ofishin don amsa tambayoyi.
Jaridar Primium time ta Nigeria ta ce komitin ya bada wannan sanarwan ne a ranar jumma'an da ta gabata. Ya kuma bukaci shuwagabannin kamfanonin da suka yi aiki da tsohon mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro tun daga shekara ta 2011-2015 da su zo da dukkanin takardun da suke da dangantaka da ofishin daga a tsakanin 12-zuwa - 26 ga wannan watan don tabbatar da sambo dusuki ya rarraba dalar Amurka bilion $2.1.
Ya zuwa yanzu dai an tabbatar da cewa Sambo dusuki ya rarraba kudaden tsakanin, yan uwa da abokai da kuma yan siyasa a jam'iyyar PDP wacce take mulki a lokacin.
Title :
Komitin Binciken Kudaden Sayan Makamai Da Aka Cinye Ya Kari Kamfani 241 Don Amsa Tambayoyi
Description : Komitin da aka kafa don binciken yadda tsohon mai bada shawara kan harkokin tsaro ga tsohon shugaban kasa Komitin da aka kafa don binciken ...
Rating :
5