Bayan kwanaki 640 da sace daliban makarantar Chibok su kimanin 219, shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya Alhamis ya bada umarnin a sake sabon bincike kan sace 'yan matan da aka yi a makarantarsu ta Sakandiren mata dake garin Chibok a jihar Borno.
Wannan jawabi ya fito ne daga bakin babban mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu.
Malam Garba kara da cewa Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gana da iyayen 'yan matan da wakilan mazauna garin na Chibok da kuma membobin masu rajin ganin an kwato 'yan matan, a fadar shugaban kasa dake Villa.
An sace 'yan matan ne cikin dare a ranar 14 ga Afrilu, 2014 a lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan.
Idan ba a mance ba, gwamnatin da ta shude karkashin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ta kafa kwamiti makamancin haka kan sace 'yan matan, mai dauke da membobi 26 a karkashin jagorancin Burgediya Ibrahim Sabo mai ritaya.
Malam Garba Shehu ya kuma kara da cewa nan bada jimawa ba mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Babagana Munguno zai bayyana sunayen membobin kwamitin binciken.
Title :
Buhari Ya Bada Umarni A Sake Sabon Bincike Kan Sace 'Yan Matan Chibok
Description : Bayan kwanaki 640 da sace daliban makarantar Chibok su kimanin 219, shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya Alhamis ya bada umarnin a sake sa...
Rating :
5