Kungiyar kwadago ta TUC ta bayyana cewa shugaba Buhari bai kyautawa 'yan Nijeriya ganin yadda yasa aka rage kobo 50 kawai a farashin mai yayin da man ke matukar arha a kasuwar duniya.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar Kwamared Babboi Kaigama da sakatare Musa Lawan suka sawa hannu kungiyar tace kamata yayi Buhari ya rage kamar kashi 40 cikin 100 na farashin mai ba wai kobo 50 ba.
Babboi yace lokacin kamfe Buhari yace ba wani tallafi da ake biya man fetir to me yasa zai ya janye tallafi??
Bobboi yace rage kudin mai na daya daga dalilan da yasa mutane da yawa suka zabi Buhari, to amma abu da yadaurewa kowa kai shine hatta gidajen man gwamnati na NNPC naira 86.50 aka ce su sayar to a ina talaka zai samu sauki ke nan.
Kwamared ya kuma nemi gwamnatin Buhari da ta gaggauta bunkasa tattalin arzikin Nijeriya ta hanyar rage dogaro da mai domin hakan na daya daga alkawarurrukan da Buhari ya daukawa 'yan Nijeriya.
Title :
Buhari Bai Kyautawa Yan Najeriya Ba - Inji TUC
Description : Kungiyar kwadago ta TUC ta bayyana cewa shugaba Buhari bai kyautawa 'yan Nijeriya ganin yadda yasa aka rage kobo 50 kawai a farashin mai...
Rating :
5