Tsohon mai bada shawara kan harkar majalisar tarayya a zamanin gwamnatin Shehu Shagari kuma kwamishinan kudi a tsohuwar jihar Kano, wato Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana cewa al'ummar Nijeriya suna dandana kudar su a karkashin gwamnatin Muhammadu Buhari duk alkawuran da ya dauka.
Dattijo Yakasai ya bayyana hakan ne a hirar da jaridar Vanguard ta yi da shi.
"Buhari ya hau mulki da manyan alkawura uku na cewa zai kawo karshen Boko Haram, yaki da cin hanci rashawa a kasar nan da kuma samar da ayyukan yi musamman ga wadanda suka kammala karatu. Wannan kadan ne daga cikin alkawuran da ya dauka.
Yanzu misali Buhari ya bada wa'adin watan Disamba domin kawo karshen Boko Haram, amma sai ga shi a kwanan nan gwamnatin tarayya ta zo tana jan hankulan al'umma cewa Boko Haram sun dito da sabon salon kai hari a wurare irin su makarantu, tashar mota, kasuwanni da sauran wuraren dake da cinkoson mutane", inji Tanko Yakasai.