Kungiyoyin 'yan tawayen Siriya za su yi wani zama ranar Laraba a Saudi Arabiya domin samun matsaya guda kafin tattaunawa da gwamnatin Assad da ake sa ran yi nan gaba.
Ana dai sa ran kimanin wakilai 100 na kungiyoyin 'yan tawayen da sojin sa kai daban-daban ne za su hadu to yin wannan ganawa, sai dai Saudiyya din ta ce ba ta gayyaci wakilan kungiyoyin da ake dauka a matsayin 'yan ta'adda ba cikin kuwa har kungiyar nan ta Al-Nursra Front.
Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da kasashen duniya ke cigaba da yin taruka da nufin lalubo hanyoyi na warware rikicin siyasar Siriya din wanda ya haifar da yakin basasar da yanzu haka ya shiga shekararsa ta hudu.
Title :
Yan tawayen Siriya za su yi taro a Saudi
Description : Kungiyoyin 'yan tawayen Siriya za su yi wani zama ranar Laraba a Saudi Arabiya domin samun matsaya guda kafin tattaunawa da gwamnatin As...
Rating :
5