Wasu mazauma garin Zaria da sauran wadanda ke makwabtaka da jagoran 'yan Shi'a, Sheik Ibrahim Zakzaky a jihar Kaduna, a jiya Asabar sun bukaci gwamnntin tarayya da ta haramta akidar Shi'a.
Kasancewar irin matsin lambar da suke fuskanta daga wurin 'yan Shi'a na kusan tsawon shekaru ashirin a Zaria, yanzu lokaci ya yi da ya kamata a dakatar da su domin sun gaji da takurar, kamar yadda mazauna yankin suka furta.
Mai magana da yawun su, Alhaji Ibrahim Mohammed Baba, ya bayyanawa majiyarmu cewa masu akidar Shia'a sun kasance tamkar su suke mulkar al'umar yankin Zaria da Sabon Gari, saboda irin matsin lambar da suke fuskanta a wurin su a duk lokacin da za su gudanar da taro.
Title :
Ya Kamata A Haramta Akidar Shi'a, Sakon Mazauna Garin Zaria Ga Gwamnatin Tarayya
Description : Wasu mazauma garin Zaria da sauran wadanda ke makwabtaka da jagoran 'yan Shi'a, Sheik Ibrahim Zakzaky a jihar Kaduna, a jiya Asabar...
Rating :
5