DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA
Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani, ya dauki wasu yara marayu harsu 60 a matsayin 'ya'yansa na cikinshi, wadanda za su ci gaba da amsa sunanshi a matsayin uba, kuma su samu cin gajiyar rayuwa kamar sauran 'ya'yan cikinshi.
Kwamared Shehu Sani ya tabbatar da hakan ne, lokacin da ya kai wata ziyara gani da ido a gidan marayu wanda ke unguwar Barnawa Kaduna.
Dan' majalisar dattawan ya kuma kai gagarumar gudummuwa ta kudi da kayan abincin ga marayun, yace ya aiwatar da hakanne domin marayun suji a jikinsu cewa suma sunada iyaye kamar kowa, sannan su shiga sabuwar shekara cikin walwala da natsuwa.
Sanata Shehu Sani ya kuma dauki nauyin wasu dalibai marayu harsu biyu wadanda suka kammala karatun sakandare, zuwa kasar China domin karo ilimi.
Sanata Shehu Sani bai tsaya anan ba, ya kuma garzaya zuwa Asibitin Saint Gerrald dake Kakuri Kaduna, inda yakai gudummuwar kayan abinci da magunguna ga marasa lafiya dake kwance a Asibitin.
Dan rajin kare hakkin dan Adam din, ya kuma biya kudin maguguna na marasa lafiya har mutum 40 nan take a Asibitin domin samun kulawar data dace.
Sanata Shehu Sani ya bayyana takaicinshi dangane da yadda gwamnotoci sukeyin ko in kula da harkar asibitoci, suna karyar wai sun samu nasarar ta fuskar kiwon lafiya, alhali sun kwashi iyalansu zuwa kasar waje domin kula da lafiyarsu a can.
Kwamared Shehu Sani wanda ya zubar da hawaye sakamakon yadda wajen kula da jarirai bakwaini ya kazamce a asibitin, ya yi alkawarin gina musu ingantaccen wurin kula da jarirai bakwaini nan bada jimawa ba.
Title :
Sanata Shehu Sani Ya Mayar Da Wasu Marayu 60 A Matsayin 'Ya'yan Cikinsa
Description : DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani, ya dauki wasu yara marayu harsu 60 a matsayin...
Rating :
5