Shugaban rundunar 'yan sanda na kasa, Solomon Arase ya bayyana cewa rundunar a karkashin jagorancinsa ta yi iya kokarinta wajen yakar cin hanci da rashawa, inda ya kara da cewa kawo yanzu rundunar ta kori gurbatattun jami'anta guda hamsin bisa zarginsu da laifukan cin hanci da rashawa da sabawa dokar aiki.
Ya kuma kara da cewa daga watan Mayu zuwa Nuwamba na wannan shekara, ana zargin karin wasu jami'ansu guda 56 da laifuka daban-daban, inda ake kan tuhumarsu.
Arese, wanda ya bayyana hakan a taron karshen shekara na manema labarai da ya gayyata a hedikwatar rundunar da ke Abuja a ranar Alhamis da ta gabata, ya kara da cewa a kokarin da yake na dawo da zaman lafiya a yankunan Arewa maso Gabas, ya aika da jami'an su sama da dubu uku zuwa yankin.
Title :
Rundunar 'Yan Sanda Ta Kori Gurbatattun Jami'anta Guda 50
Description : Shugaban rundunar 'yan sanda na kasa, Solomon Arase ya bayyana cewa rundunar a karkashin jagorancinsa ta yi iya kokarinta wajen yakar c...
Rating :
5