Kotun daukaka kara dake jihar Kaduna tayi watsi da rokon Dan Sule Lamido akan karar shi da akeyi akan cin hanci da rashawa.
Mai Shari’a HO Abiru ya tabbatar da hukuncin kotun kara ta farko wadda ta kama shi da laifin rashawa.
Dan Sule Lamido mai suna, Aminu Lamido yayi roko ga kotun daukaka kara da tayi watsi da hukuncin kotun farko wada ta kama shi da laifin rashawar Dala 40,000, wadda yake kimanin Naira Miliyan 7.96.
Aminu dai an fara Kama shi ne a ranar 11 ga watan Disamba na 2012 a filin jirgin sama na Mallam Amini Kano dake a jihar Kano, yana kokarin fita da Dala Dubu 40, bayan yaki bayyana cewa zaya fita da kudin. Sai Yayi karyata rubuta Dala Dubu Goma.
A watan Febrairu na 2013 aka fara gurfanar dashi a gaban Kotu. Daga baya, Aminu Dan shekara 34, Kotu ga daure shi a gidan Kurkuku Inda ta umurci a amshe Dala Dubu Goma (Naira Miliyan 1. 99).
Bayan haka ne Aminu yaje ya Shigar da Kara a kotun daukaka kara Inda ya roke ta data soke wannan hukunci da kotun farko tayi.
Title :
Kotu Tayi Watsi Da Rokon Dan Sule Lamido
Description : Kotun daukaka kara dake jihar Kaduna tayi watsi da rokon Dan Sule Lamido akan karar shi da akeyi akan cin hanci da rashawa. Mai Shari’a HO ...
Rating :
5