An bayyana gwamna Nasiru Ahmed El Rufa'i na jihar kaduna a matsayin gwamna daya tilo a tarayyar Nijeriya, wanda ya yi fice wajen kaunar mata da tausaya musu, da kuma sha'awar ci gabansu.
Kwamishinar ma'aikatar mata ta jihar Kaduna, Hajiyar Rabi Abdussalam ce ta bayyana hakan, lokacin da take gabatar da jawabi a wajen wani taro da aka shirya dangane da irin gudummuwar da mata za su bayar ta fuskar shugabanci da samar da tsaro, wanda ya gudana a Hotel din Delux dake tsakiyar garin kaduna.
Rabi Abdussalam ta kara da cewar, Allah ya yi wa El Rufa'i baiwa ta son mata matuka, wanda hakan ne ya sanya shi cusa mata masu yawa cikin gwamnatinshi, ya kuma yi tsayuwa irinta mai daka wajen kare muradunsu.
Kwamishinar matan ta kuma bayyana cewar a halin da ake ciki yanzu El Rufa'i ya bayyana kanshi a matsayin mataimakinta a ma'aikatar matan, kuma a kowane lokaci gwamnan bayada abokanan hulda sama da mata, wanda hakan ba karamin ci gaba bane ga matan jihar kaduna.
Lokacin da take gabatar da nata jawabin wata shugabar mata a tarayyar Nijeriya Madam Sarah Jibril, tace ko shakka babu mata nada muhimmiyar rawa da zasu taka wajen inganta harkar tsaro a kasarnan.
Title :
Gwamna El-Rufa'i Masoyin Mutane Ne'
Description : An bayyana gwamna Nasiru Ahmed El Rufa'i na jihar kaduna a matsayin gwamna daya tilo a tarayyar Nijeriya, wanda ya yi fice wajen kaunar ...
Rating :
5