DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA
An bayyana dukkanin taron dabar dake kiran kansu a matsayin shugabannin jam'iyyar APC a jihar kaduna, da cewar basu kasance komai ba face bara gurbi, tarin yayi, sannan 'yan amshin shatan El Rufa'i.
Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, shi ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da kwamitin yakin neman zaben shi ya kira a Ofishin shi dake titin Katsina a garin kaduna.
Sanata Shehu Sani wanda yake jawabi bisa ga wakilcin shugaban kwamitin yakin neman zaben shi mai suna Rabi'u Khalid, ya kara da cewar ya kamata jama'a su sani kuma su farga, tun bayan lashe zaben da suka yi a watan Maris da ya gabata, shugabancin jam'iyyar ta APC ya mutu murus a jihar Kaduna, biyo bayan dauke shugaban jam'iyyar mai suna Bala Bantex ya zuwa matsayin mataimakin gwamna, yayin da sakataren jam'iyyar ya rikide ya zama kwamishina, sannan wasu masu rike da mukamai a jam'iyyar har su sha daya aka rarraba musu mukamai a gwamnatin jihar, ya zamana cewar ofishin jam'iyyar ya koma kufai.
Kwamared Shehu Sani ya yi wannan jawabin ne, biyo bayan wani taron manema labarai da jam'iyyar APC ta kira ranar Talata, karkashin jagorancin shugaban riko na jam'iyyar mai suna Sha'aibu Idris, inda suka baiwa Shehu Sani wa'adin kwanaki 7 daya janye abinda suka kira miyagun maganganu da yake yawan antayawa gwamna El Rufa'i, ko kuma su yi masa korar kare daga jam'iyyar.
Kwamared Shehu Sani ya tabbatar da cewar, El Rufa'i ya tozarta gami da wulakanta 'ya'yan jam'iyyar APC na asali a jihar, mutane irin su Dr Hakeem Baba Ahmed, Hajiya Hafsat Baba, Isa Ashiru Kudan, Audi Makama Rigachikum, Haruna Sa'idu da sauransu da dama, wanda hakan ba karamin koma bayane ga APC a jihar kaduna.
Sanatan ya kuma bayyana yarfen da gungun bara gurbin 'ya'yan APC na Kaduna suke yi na cewar wai yana sukan tsare tsaren shugaban kasa, da cewar wannan abin dariya ne matuka, domin sunan shi a majalisa Sarkin yakin Buhari.