.
Karfe 9 saura kwata na dare agogo ya nuna,
lokacn da Munnir ya fito daga katn shagn kemis
din dake bakn titi. Rike yake da farar karamar
ledar magungunan da ya siyo. Tafiyar 'yan
dakikai ta kaishi gaba kadan rumfar masu gasa
nama da dakwaln kaji gashn zamani. Ya zabi
rusheshya aka baje masa ita a takrda aka watsa
yankakkn albasa, kabeji da tumatr, sannan aka
kunshe yaji daban duk aka hada masa su a bakar
leda.
Ya biya kudn ya karbi abnsa, ya dawo gabn
kemis inda motarsa 'Honda Acadamy' take fake
gefn titi, ya bude ya shiga tare da zuba ledojn a
kujerar mai zaman banza. Ya yiwa mota key, ya
ja ya tafi.
Da ka dubi fuskrsa kasan cike yake da farn ciki,
shi kadai yake amma fuskrsa sai bayyanar da
annashuwa take. Tafiyar minti 15 yayi bisa titi kfn
ya saki signal ya fada gefn damarsa, hanyr da ta
hada babbn layi mai dauke da jerin gidaje masu
kyau irin na zamani. Wasu na haya ne, wasu
kuwa mallakar masu hannu da shuni ne. Layin
tsit! Sai haushn karnuka kake ji, duk da dare baiyi
sosai ba. Yanayn unguwar kenan, ba mutane
masu yawan gilmawa musamman in dare yayi.
Ya kure layn kafn yayi kwana hagu ya shige wani
karamin get dake bude. Haskn fitilarsa ya haske
ko'ina, sai abnda ya fara daukar hnkalnsa watau
daukewar wutar nepa a filat dinsa kawai, alhali
akwai a ko'ina har filat din dake samansu. Yayi
fakin sosai ya kashe motar, ya kwaso ledojnsa ya
kulle ko'ina, ya nufi gdn ya bude kofar gilas yana
kira.
"Zeenah! Yaya akayi mu bamu da wuta?" shiru
yaji sai baby ke ta tsala kuka can ckn dakn
barcn. Ya danna waya ya dan sami haske, ya
wuce koridon da zai kaishi dakin. Tafe yake yana
fadin, "Zeenah! Wai barci ne ya kwasheki ko me?
Bebi na ta kuka!" kai tsaye wajn fitilar caji
(rechargeble) ya nufa ya kuna, dakn yayi haske.
Ya aje ledojn da sauri ya nufi inda take kwnce ruf
da ciki bisa gado, yace, "Zeenah wai barci ne
haka ko ciwon cikin?" ya fara daukar bebin dake
da tsala kuka. Ya zauna bakn gado yasa hannu
yana bubbuga ta, "Zeenah! Ke zeenah na dawo
nace" shiru kakeji wai malm yaci shrwa. Cike da
mamaki ya birkitota, "wai ke......"
Da kansa ya katse kansa yayi kuri yana kalln
abnda yafi komai bashi al'ajabi, wata karamar
wuka ce sabuwa fil! Tana daukar ido da kyalli,
wacce ke dabe bisa kahon zuciyar zeenah, jini
nata malala. Yana birkitota tana karasa cikawa,
aka zare ran gaba daya!
Zumbur ya miki tsaye bai gasgata idnsa ba,
kwakwlwrsa ta yamutse sosai, kansa yayi nauyi,
duniya ta fara juya masa. Ya dire bebi bisa gado,
ya juya da gudu yana kwala kira, "sister! 6ta!!"
bai iya hawa saman ba, nan ya tsaya tsakar wuri
yana kururuwa, "6ta ki fito ki gani! WA YA KASHE
MIN ZEENAH? 6ta! WA YA KASHETA??"
Ta saman bene ta leko, ganin ynda Munnir ke
kururuwa yana faduwa kasa shi ya gigita ta, ta
sauko a guje ta nufe shi ta kama ta rike, "lfya
Munnir? Menene?" ya dubeta ido warwaje sunyi
jajur! "An kashe zeenah 6ta, an kashe min
zeenah". "Inna-lillahi-wa-inna ilaihir-raji'un!" a
zatn 6ta mutuwa zeenah tayi sakamakn ciwn ciki,
don haka ta dubeshi ckn matsanancyar mamaki
tace, "ta mutu?" bata jira amsa ba tayi ckn gdn
da gudu tana sallallami.
Wayyo Allah! Abin baya ganuwa. 6ta ta rude tasa
hannu ta dauko bebi ta fito a gujnta. A falo suka
hadu, "Munnur ya haka?" hawaye na zuba jiki na
rawa yace, "ban sani ba, shigowata kenan da
mugungunan da kika rubuta" "wannan police case
ne Munnir, kana da lambar su?" ya kada kai, tace,
"ina da shi bari in dauko wayata". Ta wuce da
gudu, Munnir ya hada kai da bango krjnsa na
harbawa da sauri, "me kika yi musu suka kasheki
zeenah?" yana nan tsaye yana satatar hawaye
6ta ta dawo, bai iya kiran wayar ba sai ita ce ta
kira 'yan-sanda ta basu adireshn wajn. Munnur fa
kamar ya zare, 6ta keta rarrashnsa har 'yan-
sanda suka iso.
Bayn 'yan dakikai kaman uku da isowrsu, suka
kaisu dakn da gawar zeenah ke kwnce ciki.
Munnir dai bai iya kara ganinta ba, da gudu ya
sake dawowa falo ya zube kasa, tarajju'i yake
fadi yana maimaitawa. 6ta Rabi kabilar yarbawa
ce 'yar kimanin shekara 51. Tare take da 'yan-
sanda tana goye da bebin a baynta. Masu daukar
hotuna nata dauka, masu binciken dakin nayi.
DPO ya dubeta yace, "ina mijnta?" "gashi can a
falo". Ya fito ya sameshi a falon. Ji yayi an dafa
kafadrsa, ya juyo ido jazur! DPO ne tsaye, yace,
"i'm sorry, matarka ta riga ta rasu, amma ina son
ka dan natsu ka bamu hadn kai don sanin ynda
abin ya faru, hakan shi zai taimaka mana mu
binciko wdnda suka aikata wannan mummunan
laifn. Taso ka zauna" ya kamoshi ya zaunar bisa
kujera, ya goggoge hawaynsa, DPO yace, "menene
cikakkn sunanka?" "Munnir Mu'azu Shika, kuma
ina aiki da hukumar ruwa ta jiha" "sunan matrka
fa?" "Zeenah Zubairu Matazu" hawaye suka wnke
masa fuska, yasa tafukn hannaynsa ya rufe
fuskar. DPO yace, "hakuri zakayi Munnir, ina so
ka gaya min barayi ne suka shigo ko kuwa ya
abin ya faru?"
Murya na rawa yace, "ni fa ban sani ba. Zeenah
ta haihu yau misaln karfe 7 na daren nan.
Wannan 6ta Rabi ita ta amshi haihuwar, kuma
makwbciyarmu ce ita ke filat din samanmu. Byn
ta haihu ta gama gyara bebin, sai ta rubuta
magnguna da allura tace inje in siyo sbd ta samu
tashia, don taji karfn jiknta, ga kuma ciwn ciki da
take yi. Duka-duka da fitowata da dawowata bai
wuce minti 45 ba, ina zuwa naga ko'ina da wuta
amma gdnmu babu, abn ya bani mamaki. Da na
shiga ina ta magana bata amsa ba, ga bebi nata
kuka ita kuma tana kife ruf da ciki, shine na
birkitota, kawai abnda idanuwana suka nuna min
kenan, Zeenah ckn jini ga wuka soke a kahon
zcyrta..
Ya goce da kuka. 6ta da ke tsaye baynsa ta dafa
kafadnsa biyu tana jijjigashi, ita ma kukan take yi,
"yi hakuri munnir, yi hakuri" DPO yace, "lokcn da
ka fita babu kowa a ckn gdn, kuma ba ka lura da
wani ko wasu a harabr nan eriyar ba?" ya kada
kai, "ita kadai na bari, 6ta ma tana rubuta min
magngnan ta koma filat dnta tace zata je ta
dauraye jknta kafn in dawo. Sannan banga kowa
a eriyar nan ba, ko akwai su ma to sun boye, ni
banga kowa ba" DPO ya dubi 6ta yace, "ke ma
baki ji motsi ko ihu ba bayn fitar munnir?" tace,
"gskya banji komai ba, illa fitarsa da mota, haka
da ya dawo naji tsayuwar motrsa. Abnci nake ci a
time din da ya shigo, shi yasa ban fito yi mata
allurar ba. Sai kuma naji ihunsa yana kirana"
DPO yayi shiru, al'amarn ya caja masa kai, duk
da ya saba ganin cases irin wadannan. Ya nisa
kfn yace, "akwai alamar an dan yi dambe da ita
kfn aka kasheta, sbd dan karamin kafet din dake
shimfide ya tattare gefe guda, haka kuma
shmfidar gadn, ga kuma filo a kasa. Amma akwai
wasu ledoji guda 2 a gefe, dama a dakn suke ko
kuwa ba naka bane?" yace, "ni na shigo dasu.
Daya magnguna ne cknsa, guda kuma kaza ce na
siyo mata" yace, "ok. To ita wutar nepan mita
daya gareku ko kuwa kowanne filat da mitar sa?"
yace, "kowa da mitarsa" "ina naku take?" "gata
nan a koridon waje" "muje in ganta"
Suka mike suka fito, DPO ya haska da tocila,
kawai kashewa akayi. Ya dubi munnir yace,
"kashe mitar akayi, ina so a barta a haka, sai
mun gama bincike" yace, "shi kenan". Suka juyo
suka dawo ckn faln, kfn DPO yace, "munyi waya
ynzu ambulnce zata zo a dauki gawar zuwa
asibiti likita ya duba ta"
Munnir bai ce komai ba, suka ji jiniyar motar
asibiti ta shigo harabar gdn. Suka shigo gadan-
gadan daukar gawa. Jimawa kadan aka fito da
gawar lullube da farin yadi, amma kan kace me
jini ya lalata ta face-face. Suka rankaya asibiti
tare da 'yan-sanda 2 da munnir, da 6ta tana goye
da bebi. Sauran 'yan-sandan kuwa aka bar su
ckn gdn, don ci gaba da bincike. A ckn asibiti
kafn likita ya gama binciknsa munnir ya karbi
wayar 6ta ya kira wasu lambobi, lokcn karfe 11
na dare. Ba'a jima ba aka dauka, "hello!" hawaye
suka tsinke masa, baki na rawa yace, "yaya an
kashe Zeenah......." ya sarke da kuwa, ya cire
wayar ya fadi kasa magashiyyan. Aka amsa daga
daya bangaren "hello! Wa ke magana? Ban gane
kan zancen ba" 6ta tace, "Munnir ne ya kira.
Kuda dai abn babu dadin ji, bayan ta haihu din
nan ya fita sayo magana. Wlh kafn ya dawo wasu
suka shiga suka kashe Zeenah" yace "iye! Ban
gane ba? Ba dazu yayo waya yace ta haihu ba?"
ta sake yi ta sake yi masa bayani, duk da tasan ba wai bai
gane bane, a'a rudewa yayi". Ai kuwa ya aje
wayar ya dauki salati. Juwairah ta kara zaro ido,
"me ya faru baban sultan?" bai tanka mata ba ya
nufi kofar falon ya bude, ta biyo shi. Ya sakko
benen da gudnsa zuwa tsakar gida, sannan ya
zare sakatar kofar da ta raba sassan biyu, ya fice
ckn hnzarnsa, ta biyo shi itama. Gaban kofar faln
ya tsaya yana bugawa, ckn kosawa da zakuwa a
bude. Jimawa kadan aka bude, "menene
Abdullahi?" yace, "Baba matar Munnir ta rasu!"
daidai lokcn mamansu na tsayawa waje, gaba
daya suka dauki salati, kafn alhajn yace, "amma
yace ta haihu lfya lau! Shi yasa ma nace a bari
sai da safe a tafi" "wai kasheta aka yi" "barayi?"
ya tmbaya. Nan dai ya bayyana musu kamar
ynda 6ta ta gaya masa. Take nan juwairah ta
ynke jiki ta fadi a sume. Mama ta nemo ruwa
suka fara antaya mata, da kyar ta dawo
hayyacnta. Ta fashe da kuka tana kwarara salati.
Mama na yin nata hawayen hawaye na zuba.
Abdullahi yace, "baba menene abnyi ynzu?" yace,
"zuwa zanyi in gayawa mahaifnta, sai inzo mu
tafi kaduna" yace, "to amma kana ganin babu
matsala idn ka dumfari alh. da wannan
maganar?" yace, "ya zama dole Abdullahi, ba
mahaifnta bane? Ya zama wajibi a gaya masa
domin hakknsa ne, saura kuma ya rage nasa. Ina
zuwa".
Ya kama hanya ya fita, Abdullahi ya zauna ya
kama kai sbd kan nasa ya dau zafi, yace, "kai
jama'a! Allah na tuba, wannan kuma wace irin
kaddara ce ta fado mana? Hasbunallahu wa
ni'imal-wakil! Ya maimaita sau uku, hawaye suka
tsunke masa ya shiga sharewa yana kara salatin
manzo ckn ransa. Alh. Mu'azu ke ta buga kofar
gidan da ke kalln nasa, ya jima yana bugawa kfn
yaji murya ana tambaya, "wanene?" "alh. Mu'azu
ne" "lfya?" ya amsa, "babu lfya alh. Zubairu, kayi
wa girman Allah ka bude kaji" "ba zan bude ba!
Kuma daga rana mai kamar ta yau ka sake zuwa
a irin wannan lokaci ka buga min kofar gida sai
na ci mutncnka, Sannan in sa a wulaknta ka a
garin nan" "abin bai kai haka ba, kuma karshn
magana zuwa nayi in gaya maka Allah ya yiwa
Zeenah rasuwa, mu zamu wuce kadunan yanzu"
Ai da sauri ya zare sakata ya fito, a lokcn har
alh. Mu'azu ya juya ya fara tfya, "me kace?" ya
tambaya ckn zafn rai da masifa. Ya juyo ya
dubeshi, "ynzu aka yo waya an shigo har ckn
dakin barcnsu an kasheta, Munnir ma baya nan
ya tafi siyo mata magunguna......" ai yana sa aya
yaji ya cakume shi, "idan kun isa Allah ya tsine
min? 'Yar tawa guda daya? Har kana iya gaya
min Munnir din baya nan, watau kana kare danka
ko? To na rantse da wanda ya halicce nh ba zan
yarda ba. Sai ya nemo min wnda ya kashe min
'ya"
Hajiya saratu ta fito, "wai menene haka da
tsohn daren nan?" ta kama hannun mijnta ta
banbare da kyar, "me ya faru alh. Mu'azu?" ya
maida mata sakon da suka sake samu bayn na
haihuwar Zeenah. Bata gama ji ba ta zube
sumammiya, alh. Mu'azu ya juya ya shige gdnsa,
ya bar alh. Zubairu na ta masifa. Makwbta suka
fara fitowa sbd kwakwaznsa, gashi da murya
kamar tashn hnkali. Su suka taimakawa h. Saratu
ta farfado, ta shiga rusa kuka tana sallallami.
Kowa yaji abnda ya faru sai hnkalnsa ya tashi.
Alh. Zubairu kuwa ofisn 'yan-sanda ya nufa. To
wa zasu kama? Domin kuwa kafn ya dawo da
'yan-sandan su alh. Mu'azu sun damkh hanyar
kaduna misaln 11:30 na dare. H. Saratu taso
binsu, amma alh. Mu'azu yaki amincewa yace ta
jira mijnta su taho tare. Yana isowa ya tarar sun
tafi, take nan ya karawa 'yan-sandan kudi , yuu
suka bishi a motarsa suma suka nufi kadunan.
Da yake gudu suke yi ba ji ba gani, ga titi ba
kowa, karfe 12:20PM su alh. Mu'azu na shiga
harabar gdnsu Munnir, kamar ynda ya gaya musu
a waya cewar sun dawo gida, amma gawa na
mutuware. Yana tare da DPO da wasu 'yan sanda
2 har zuwa wannan lokcn da suka iso. Munnir ya
fito ya kara fashewa da kuka, suka kamo shi
suka shiga dakin suka ga ynda ya baci da jini
ko'ina, hnkalnsu ya kara tashi, alh. Mu'azu kansa
sai da ya zub da hawaye, sbd tsabar tausayin rai!
Ya fito da sauri ya dawo falo ya zauna. Shiru
kafn yace, "kuma babu abnda aka dauka a ckn
gidan?" DPO yace "ba'a dauki komai ba, shi yasa
muke zatn dama can kisan ya kawo su" "to ynzu
ina bincike ya tsaya?" "abnda muke kan yi kenan
alh. Kuma in Allah ya yarda za'a gano wadnda
suka aikata laifin" yace, "Allah ya yarda, ya tona
asirnsu. Akan wannan maganar bana son kuyi
sanyi yallabai, ko nawa ne zan kashe idn za'a
gano wnda ya kashe wannan baiwar Allah. Me
tayi musu? Wannan yarnya da babu ruwnta da
kowa? Kila kuma Munnir din aka so kashewa,
basu sameshi ba suka kashe masa mata"
DPO yace, "ba yadda ba zata kasance ba,
amma ka kwntr da hnkalnka alh. Sai inda
karfnmu ya kare". Yana sa aya motrsu alh.
Zubairu na tsayawa, duk suka mike, 'yan-sandan
da ke tare da su suka yi kwntan bauna. Alh.
Zubairu ya fado faln kamar mahaukaci tare da
'yan sandan da ya kwaso, bai tsaya wata-wata
ba ya nuna munnir, "ga matsiyacin nan, ku kama
min shi nace!" 'yan-sanda suka zaburo suka nufo
munnir da ke tsaye sototo yana kalln ikn Allah.
DPO da yaransa suka fito, "yaya lfya?" alh.
Zubairu yace, "ba ruwanka malam, ku kama min
shi, sai ya fadi yadda yayi ya kashe min 'ya" DPO
yace, "kasan da wa kake magana?" ya ciro I.D
card dnsa ya nuna, "kar ka kawo mana zafin kai
anan, a bakn aiki muke". Ya juya kan 'yan-sandn
da suka kama munnir yace, "ku sake shi!" Dole
gaba da gabnta, suka sake shi kuma suka sarawa
oga. DPO ya dubi alh. Zubairu, "kai ne mahaifn
zeenah?" "ni ne" "to kayi hakuri ka zauna ka bani
hnkalnka muyi magana ta fhmta" dole alh.
Zubairu ya saduda ya koma da baya, ya jingina
da bango yana maida numfashi. Ido jawur! yace,
"ku gama naku, nima zanyi nawa, domin wannan
hadin baki ne" DPO yace, "sbd me kace haka?" ya
nuna su alh. Mu'azu yace, "kaf! dinsu nan da
kake gani makiyana ne" mamaki ya kama DPO,
"to ya akayi 'ya'ynku ke auren juna?" "fin karfi
aka yi min, amma Allah na gani ba da yawuna
akayi auran nan ba. Yaron nan ya riga ya hure
mata kunne, yasa ta bijire min, ya hanata zama
gidan mijin da na bata, ashe da manufarsu, so
suke su kashe min ita" DPO yayi dan shiru yana
nazarn maganganun alh. Zubairu, kafn yace,
"kana ganin munnir zai iya auran zeenah domin
ya kasheta? Kar fa ka manta yau din nan ta
haihu. Ya kasheta ya bar jaririyarsa ckn maraici
abu ne ma yuwuwa?" ckn fada yace, "babu abnda
ya dameni da wannan, abnda kawai na sani shine
'yata nake son gani, ko kuma ya amsa laifnsa tun
bai hadu da fushina ba. Ba zan hakura ba, ba zan
lamunta ba, ba kuma zai motsa ko nan da can ba
sai ya fadi ynda yayi ya kashe min 'ya..
Zubewar da munnir yayi kasa a sume shi ya
kwashe hankaln kowa zuwa gareshi. Alh. Mu'azu
ya tarairayo shi bisa jknsa, ya dubi abdullahi
yace, "kawo ruwa abdullahi?" ya shiga kicin da
gudu ya bar alh. Zubairu na fadin, "ka gama
sumanka yaro ka farfado, ina nan yau babu fashi
ko ni ko kai!" DPO yace, "ka saurara mana alh. Ai
kayi bayaninka, ba shi kenan ba? Bincike kuma
ka barshi a hannun mu, babu abnda zai gagara"
yace. "na kyale sbd kai kana wajn nan, amma wlh
ba don haka idan sama da kasa zasu hadu, ba
zan taba yarda ba, sai dai ayi kare-jini-biri-jini.
Ai sun sanni wli bani da kyau!" DPO ya zura masa
ido yana ta kara fahmtar lafuzznsa inda suka
dosa. Ya kada kai yace, "to shi kenan, ynzu dai
gawa na mutuware, abnda nake so da kai shine,
ayi hakuri abi maganar ckn natsuwa da ilimi, don
a gano mai laifi". Ya gyara zaman malummalm
dinsa, babu 'yar ciki sai farar singileti, yace, "a
wane asibitin take? Zan biya in dauka mu wuce
zariya, gobe ayi mata sutura". Sai a lokcn alh.
Mu'azu ya tanka masa, "a'a wannan kuma hakkin
mijnta ne. Alh. Zubairu mu ne......" "ku ne me?
Ku ne kuka kasheta kuja kuce zaku yi mata
sutura? Ba zai yiwu ba! Allah ya tsine ma wnda
ya taba min gawar 'ya. Azzaluman mutane
matsiyata. Yallabai wane asibiti kuka kai gawar?"
alh. Mu'azu zaiyi magana munnir dake kwnce
jiknsa ya rufe masa baki ya girgiza kai. DPO ya
bashi amsa, "wahala zakayi alh. Ko na gaya maka
kaje bazasu baka gawar nan ba sai da sa hannun
mijnta, don shi yasa hannu a takardun" yana huci
kamar mesa ya dubi su alh. Mu'azu, "zamu hadu
a zariyan, ku a zariyan, ku daukota ku zo da ita, amma sallah
ban lamunce muku ba!" ya shura takalmansa ya
fice. 'yan-sandan da ya zo da su suka mara mai
baya, ba tare da wani ckn su alh. Mu'azu ya
tanka masa ba.
DPO ya matsa kusa da munnir ya tsuguna
yace, "akwai maganar da ya kamata muyi da kai
munnir". Ya runtse ido numfashnsa na wucewa da
kyar! Baya son yin magana, sbd tsananin zafn da
zcyrsa take masa, ya kada kai kawai ya kasa
furta komai. Abdullahi ne yace, "ranka ya dade ka
dan yi masa afuwa zuwa gobe, dubi ynda
numfashnsa ke tfya" yace, "shikenan, ni zan
koma, amma zan bar yarana guda 2" alh. Yace,
"ba laifi mun gode" ya sa kai ya fice ya bar 'yan
sanda guda 2. Alh. Mu'azu da Abdullahi tare da
6ta kadai ke ta maida maganar, shi kuwa munnir
tuni ciwo mai zafi ya kama shi, wnda shi kansa
ba zai iya cewa ga inda ke masa ciwon ba. A
haka har aka kira assalatu babu wnda yayi ko
gyngyadi! Munnir kam sai da abdullahi ya mikar
da shi, ya rike ya raka shi bayi ya yo alwala, ya
yi sallah. Ckn sujada ya mika rnknsa wajen
Ubangiji da ya tona asirin duk wnda yake da
hannu a kisan matrsa. Fuskarsa sharkaf da
hawaye ya dago sujada, yayi zaman tahiya
sannan ya sallame sallar. Kafn su munnir su fito
zancen ya bazu huguwa, makwbta suka yi dafifi a
kofar gidan don yi wa munnir jaje. Da dama daga
cknsu kuka suke yi, duk da basu ga gawar ta ba,
musamman wadnda suka san zeenah kuma suke
huldar mutnci tun zuwanta unguwar shekara daya
da wata hudu kenan.! Karfe 7 Suka rufe gidan
suka wuce asibiti, suka bar jama'a da jimami tare
da tausayawa ga 'yar jaririyar da aka bari. Gawar
suke so a basu don yi mata sutura. Kamar ba za
a basu gawar ba, kai ka rantse da Allah ba su
suka kawota jiya ba. Duk da 'yan sanda, amma
turanci yaki karewa, da kyar da zufar goshi suka
sami gawan. Karfe goman safiya mama ta bugo
waya don jin halin da ake ciki. Ita ke basu labarin
bakar wainar da alh. Zubairu ke toyawa tun daren
jiyar har zuwa wayewar garin yau.
Ai kuwa sun iske badakalar, domin isowarsu
ke da wuya alh. Zubairu ya tsare, Allah kashe shi
ba zasu shiga da gawa ckn gdnsu ba. Ga dumbin
jama'a da suka taru, mafi yawansu dangn
mahaifiyar zeenah ne daga rimin tsiwa ckn birnin
zariya. Amma hakan bai hana alh. Zubairu
kwakwazn da yake yi ba, tare da kumfar baki a
dole sai a bashi gawar 'yarsa. Babu wnda bai ba
haushi ba, mutum kullum baya neman zaman lfya
sai tashn hnkali. In banda son zcya, yarnya ta
mutu yace ba za'a kaita dakn mijnta ayi mata
sutura ba? Mecece hujjrsa ta yin hakan? Kuma an
taru ana gaya masa gaskiya amma yaki ji, shi
kuwa alh. Zubairu wani irin mutum ne? Me yayi
zafi mai tsanani haka tsakanin gidajen biyu?
Alhalin har zuri'a ce a tsakanin su? Akwai
magana! Wannan bambami na alh. Zubairu yayi
yawa. Munnir barin wajen yayi ya shiga falnsu,
sbd bakn cikn kalaman da suruknsa ke fadi,
kowacce kalma karawa zcyrsa ciwo take yi, ji
yake tamkr ya hadiye zcya ya bi zeenah, don a
ganinsa babu sauran wata ragowar jin dadi da
zaiyi nan gaba. A falon mama ta iske shi, bai iya
ce mata komai ba, kawai kuka ya fasa, ta jawo
kansa jiknta murya na rawa tace, "kayi hakuri
munnir, haka Allah ya so, iya kwanakin zeenah
kenan a duniya. Alkawari ne baya tashi, duk iya
soyayyar da kake mata ubangiji ya fi ka son
kayan sa. Ka yi imani, ka dake zcyrka kaji?" ya
dago fuska ya dubeta, gaba daya ya sauya
kamanni, yace, "mama yanzu ina amfanin tijarar
da alh yake yi? Mutuwar zeenah bata ishe shi
ishara ba? Ya ma bari a mata sutura abin ya
gagara, sai zage-zage yake akan gawa. Me
zeenah ke bukata ynzu bnda zuturta ta? Wace
irin kiyayya alh ke min wacce gawar zeenah ba
zta sa ya saduda ba?" ta goge kwalla tace, "ka
bar maganar nan munnir, sanin kanka ne auran
ka da zeenah Allah ne ya kulla shi, don alh.
Zubairu yayi fada akan gawa ba abin mamaki
bane. Babanku ma yace a bar masa gawar ya
dauka, idan sun gama shryata suka fito da ita,
kwa je ku sallace ta". Yayi zuru wasu hawayn
suka silalo masa. Ta kara cewa, "babu komai,
addu'a kawai zeenah tafi bukata, a duk inda kake
kayi mata, in sha Allahu rahma zata je gareta.
Kayi hakuri". Haka tayi ta rarrashnsa, ji kawai
yake yi amma bakin ciki kamar ya kashe shi.