$IFI_$IFI
___%___
*fulawa
*dakakken nama
*kwai
>attaruhu,albasa
>magi,gishiri
>yeast
~garin tafarnuwa
~curry
~butter
Zaki kwaba fulawar ki da yeast da dan magi da curry da kuma butter,sai ki bata kamar minti 30 haka,dama kin daka namanki bayan kin dafashi da albasa da magi da garin tafarnuwa,sai ki jajjaga attaruhu da albasa ki zuba a ciki kisa maggi,gishiri da curry da tafarnuwa ki jujjuya,
san nan ki dauko fulawar nan ki dinga yanka kina murzawa,amma kiyi saman me fadi kasan kuma siriri yadda ze nadu sosai sai ki dauko wannan hadin ki dinga diba kina zubawa akan wajan fadin dama kin dafa kwanki kin bareshi kinyi masa yanka (slice) sai ki zubashi shima sai ki dinga nadewa har ya nadu sai ki danneshi da jelar cokali yadda ze zauna sosai,sai ki dauko kadadden kwanki ki shafa a jiki,sai ki gasa a oven,
amma idan ze kwana karki saka masa kwai kuma ki soya naman tukunna.
Asma'u Garba