* Fulawa ko cabbege
* Nikakken nama
* Butter
* Albasa,Attaruhu
* White pepper
* Curry
* Baking powder
* Maggi,Gishiri
* Mai
Idan da fulawa zakiyi sai ki tankadeta kwabata baking powder da butter magi gishiri,kamar kwabin meat pie,ki barshi kamar 30mins,
ki dauko namanki da kika daka ki tare da albasa da attaruhu sai ki soyashi ki zuba curry magi white pepper da albasa idan suka soyu ki sauke,
sai ki dauko fulawar nan ki murzata tayi fadi,
ki fitar mata shape da bakin kofi,amma babba sai ki dinga zuba naman kina nadewa kamar nadin takardar tsire,sai ki soya...
Asma'u