Alalan waken soya
~~<>~~<>~~<>~~
• waken soya
• shinkafa
• magi&gishiri
• curry
• attaruhu
• albasa
• hanta
• kwai
• mai
• kifi
ki jika waken soyarki idan ya jiku ki regeshi ki kai a nuko miki in annuka ki tace shi ki fidda dusar sai ki kawo garin shinkafarki ki zuba aciki yadda zeyi kauri kamar kullun alala ki kawo soyayyen kifinki da kika gyara ki zuba a ciki ki yanka dafaffiyar hantar ki kanana tare da kwai ki zuba a ciki,
sai ki fasa wani kwan ki zuba a ciki,tare da magi gishiri curry da mai wanda kikeso ja ko fari,sai ki jujjuyasu sai ki zuba a gwangwani ko leda ki dafa,yana da dadinci a baki kuma yana da amfani a jiki ki gwada ''yar uwa