FANKE ME KWAI
_____________
• kwai
• madara ta ruwa
• flawa
• suga
• yeast
• mai
ki kwaba fulawar ki da yeast da madara kamar kwabin fanke amma ya danyi kauri sai ki barshi zuwa 30 mins dama kin dafa kwanki kin bare iya adadin da kike so sai ki dauko kullun ki dinga tsoma kwan a ciki fulawar ta kama ko ina kina soya wa a mai me zafi zakiga yana tashi kamar fanke harki gama,idan kuma me gishiri zakiyi sai kisa wa kullun maggi curry jajjagaggen attaruhu,
Note:da dama ana tambayar mu kan darussan da mukayi a baya dama abubuwanda bamayinsu a wannan dandali kamarsu alawar madara kwakumeti su charbin malam gyaran jiki dadai sauransu,to gaskia ko zamuyisu sai dai mu ware musu ranakun da zamu dinga kawowa amma ba kullumba,kuma akwai wadanda suke bukatar maimaici na wani darasin da ya wuce? sai munji daga gareku.
Asmau Garba.