Yadda Sheikh Lawal Mai Guduma ya rasu da kuma wasiyyar da ya bayar ana gobe zai rasu
Daruruwan jama’a suka yi dafifi a filin masallacin idin mai martaba Sarakin Gombe domin gudanar da Sallar jana’izar margayi, Sheikh Lawal Mai Guduma wanda Allah ya yiwa rasuwa tare da diyarsa.
Shehun malamin ya rasu ne a hadarin mota da ya rutsa da shi a Dikku da sanyin safiyar ranar Asabar lokacinda yake kan hanyar komawa Gombe bayan kammala wani wa’azi da ya gudanar a karamar hukumar Kibiya ta jihar Kano a daren ranar Juma’a.
A wani bincike da HAUSA TIMES tayi ta gano cewa su Biyar ne a cikin Motar lokacin da tayi hadari, Matarsa da diyarsa da kuma Muridansa Biyu,
Shi da diyarsa Khadija yar shekara Uku sun rasu a wani Asibiti dake garin Dikku a yayinda Matarsa Halima ke jinya a Asibitin FMC Gombe sai Muridansa wadanda tuni har sunji sauki an sallamesu.
Dan kimanin shekara 46 Mallam Lawal Mai Guduma ya rasu ya bar yara Takwas da mata Biyu da almajirai da dama.
Wani babban dalibin mai suna Sheikh Sheriff Saddiq Auwal sa ya shaidawa HAUSA TIMES yadda rasuwar ta kasance da kuma wasiyyoyin da Malam ya bari ana Gobe zai rasu,
Yace “Malam ya taso wa’azi daga Kibiya misalin karfe daya na daren ranar Juma’a, shi da Matarsa da diyarsa da Muridansa Biyu wadanda ke tuka shi, sun yi Sallar Asubahi a garin Daraoza daga nan sai yace shi zai tuka motar, sun wuce Dikku sai Allah ya kaddara hadarin su wajajen 7:00 na safe. An kai shi Asibiti a cen Dikku amma sai rai yayi halinsa wajajen karfe 7:30 na safiya. “
A cewar Sheriff ” Wata karama da Mallam ya nuna shine, kamar an sanar dashi rasuwarsa, domin a ranar Juma’a da yamma ya kira wayar almajirinsa yace ya bawa ‘yayansa su gaisa bayan sun gaisa sai yace a bawa babban dashi Auwal Dan kimanin shekaru 12″
Sai yake yiwa Dan nashi wasiyya cewa idan ya mutu a dauki Haraminsa na Umarah ayi masa likafani dashi sannan a binne shi a wani daki da yake yiwa yara karatu sannan dansa Saddiq shi zai fara zuba masa kasa sau Uku idan an kwantar dashi a kabari” inji shi
Daya daga cikin ‘Yayan sheikh Dahiru Othman Bauchi, Sheikh Muhammad Katihu ne ya sallaci gawar margayi Lawal wacce akayi a mota sakamakon cikowar mutane. HAUSA TIMES ta gano cewa daga cikin manyan malaman da suka halarci jana’izar sun hada da Muhammad Kopwa Halifan Shehu Manzo da Sheikh Muhammad Tijjani khalifan Shehu Bolari da Sarkin Bolari Alhaji Garba Abubakar Hakimin Bolari da kuma babban sakataren Gwamnan jihar Gombe, PPS Alhaji Dr. Sani sai Honorable A. A Haruna wani tsohon Dan majalisar dokokin jihar.
A halin yanzu ana cigaba da karbar ta’aziyyar margayin a gidansa dake Unguwan Yelwan Guruza a jihar Gombe.